“Talaka Ba Ya Ci”, Gwamna Ya Yi Fatali da Saka Kwai a Jerin Abinci da Zai Ragewa Farashi

“Talaka Ba Ya Ci”, Gwamna Ya Yi Fatali da Saka Kwai a Jerin Abinci da Zai Ragewa Farashi

  • Gwamnan jihar Akwa Ibom ya kawo tsarin siyar da abinci mai rahusa ga al’ummar jiharsa saboda rage musu wahalhalu
  • Gwamna Umo Eno ya tabbatar da hakan ne yayn da ya sanya wa dokar hannu domin samar da abinci mai rahusa
  • Sai dai gwamnan ya ki amincewa da bukatar sanya kwai a cikin jerin abincin inda ya ce talaka bai cin kwai bare a saka a ciki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Akwa Ibom – Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya ki amincewa da saka kwai a cikin kayan abinci da gwamnati za ta siyar a farashi mai rahusa.

Gwamnan ya ki amincewa da rokon da aka yi na saka kwai din inda ya ce talakawa ba su cin kwai.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya girgiza Intanet ta hanyar daga buhun shinkafa da hakoransa

Gwamna a Najeriya ya yi fatali da kwai a tsarin abincin da zai rage musu farashi
Gwamna Umo na Akwa Ibom ya ce talaka bai cin kwai domin haka bai tsarin abinci da zai siyar a farashi mai rahusa. Hoto: Umo Eno.
Asali: Facebook

Jerin abincin da za a siyar da sauki

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya sanyawa dokar hannu domin siyar da kayan abinci mai yawa cikin farashi mai sauki, cewar TheCable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga cikin kayan akwai shinkafa, wake da garri wanda za a siyar a kowane wata sau daya ga jama'ar jihar.

Wani daga cikin wadanda suka halarci taron ya ba da shawara inda ya ce shinkafa da garri nau’in abinci ne masu kara karfi inda ya ce mai gina jiki wake ne kadai.

Ya ba da shawarar saka kwai domin a samu nau'in abinci mai gina jiki su zama biyu, amma gwamnan ya yi watsi da shawarar, a cewar Premium Times.

Martanin gwamnan kan saka kwai a abinci

“Talakawa basu cin kwai, ya kamata mu duba a bincin da suka fi ci domin saukaka musu inda ya nuna shirin ba mai dorewa ba ne.”

Kara karanta wannan

Gwamna ya fadi halin kunci da ya ke ciki, ya ce shekaru 2 bai samu albashi ba, ya yi tone-tone

“Dukkanmu mun sani akwai yunwa a kasar nan, mutanenmu su na bukatar abinci domin haka a matsayinmu na gwamnati muke son kawo agaji a bangaren.”
“Hanya daya da za mu yi haka ita ce samar da cibiya da za ta tabbatar da ba da abincin cikin farashi mai sauki ga jama’a.”

- Umo Eno

An fara siyar da abinci mai sauki

Kun ji cewa Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya sanar da kasuwannin da za a samu abinci mai sauki.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya rage farashin abinci da kaso 25 domin tallafawa al’ummar jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.