Kano: Gwamna Abba Kabir Ya Yi Fatali da Umarnin Kotu, Ya Rusa Wasu Gidaje a Watan Azumi
- Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta take umarnin kotu, ta ci gaba da rusau a yankin ƙaramar hukumar hukumar Kunbotso
- Hukumar tsare-tsare da raya birane ta Kano KNUPDA ta rushe wasu gidaje a garin Gurin Gawa ranar Lahadin da ta gabata
- Lauyan waɗanda lamarin ya shafa ya nuna damuwa kan yadda gwamnati ta yi watsi da umarnin kotu, ya ce za su ɗauki mataki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Wasu mazauna garin Gurin Gawa da ke karamar hukumar Kumbotso sun rasa matsuguni yayin da motar rusau ta gwamnatin Kano ta dira kan gidajensu.
A ranar Lahadi ne hukumar tsare-tsare da raya birane ta jihar Kano (KNUPDA) ta rusa gidaje da dama a garin, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Wannan rusau dai na zuwa ne duk da umarnin babbar kotun jihar Kano, wadda ta dakatar KNUPDA daga rusa gine-ginen al'umma a yankin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake zantawa da manema labarai a ranar Lahadin, lauyan da ke kare masu kara 23 a rikicin, Abubakar Alhaji Rabi’u Doka, ya ce wadanda yake karewa sun samu umarni daga babbar kotun jihar.
Sai dai a cewarsa duk da wannan umarni na kotu, gwamnati karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta yi fatali da shi, ta aikata abin da ta yi niyya.
Wane mataki mutanen ke shirin ɗauka?
"Waɗanda nake karewa sun samu umarni daga babbar kotun jiha kuma mai shari'a Aisha Ibrahim Mahmoud ce ta jagorancin shari'ar. Kotun ta umurci KNUPDA ta dakatar da rusau."
"Sai dai kuma abin ban mamakin shi ne KNUPDA ta yi watsi da umarnin kotu, ta ci gaba da rusa gine-ginen.
"Domin ɗaukar mataki, masu shigar da kara suna shirin fara tuhumar raini, suna ganin cewa kin bin umurnin kotu da KNUPDA ta yi ya janyo musu hasara mai yawa."
- Abubakar Alhaji Rabi'u.
Lauyan ya ƙara da cewa waɗanda yake wa aiki sun mallaki filaye kusan 32 da rusau ta shafa kuma suna da niyyar neman diyya ta hanyar doka, Daily Trust ta ruwaito.
Manajan darakta na KNUPDA, Ibrahim Yakubu Adamu, bai amsa kira ko sakon tes da aka tura masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto a jiya.
Gwamna Abba ya yi nasara a kotu
A wani rahoton kuma Babbar kotun tarayya ta yanke hukunci kan ƙarar da aka nemi hana Abba Gida-Gida naɗa ciyamomin rikon kwarya a kananan hukumomin Kano.
Alkalin kotun mai shari'a Abdullahi Muhammad Liman, ya kori ƙarar a zaman ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, 2024.
Asali: Legit.ng