Ramadan: Dan Takarar Shugaban Kasa Na LP Ya Ziyarci Musulmi an Yi Buda Baki da Shi

Ramadan: Dan Takarar Shugaban Kasa Na LP Ya Ziyarci Musulmi an Yi Buda Baki da Shi

  • A yayin da al'ummar Musulmi ke kokarin yin buda baki, an hango Peter Obi a cikin wani masallaci yana cin abinci da wani karamin yaro
  • A cewar wanda ya dauki bidiyon, dan takarar shugaban kasar a 2023 ya aikata hakan ne domin nuna kauna ga mabiya addinin Musulunci
  • Sai dai da alama hakan bai yi wa wasu dadi ba, yayin da wasu ke dangana hakan da siyasa, wasu na ganin bai kamata ya je masallacin ba

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour (LP) a zaben 2023, Peter Obi, ya bi sahun Musulmi a babban masallacin Juma’a na Maraba-Nyanya a Abuja domin ayi buda baki da shi.

Kara karanta wannan

Yadda rikicin gona ya yi sanadin kashe sojoji 17 a jihar Delta, in ji shugaban al'umma

A cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa a shafin X (Twitter a baya), an ga tsohon gwamnan jihar na Anambra ya zauna kusa da wani yaro akan tabarma suna cin shinkafa a kwano daya.

Peter Obi ya ziyarci Musulmi a musallacin Abuja
Ramadan: Yan Najeriya sun yi martani kan zuwan Peter Obi masallacin Abuja.
Asali: UGC

Faifan bidiyon ya kuma nuna kusan mutane 1000 a masallacin suke buda baki yayin da wasu ke kallon yadda dan takarar shugaban kasar na LP ke ciyar da yaron.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da wani a masallacin ya ce

Ana iya jiyo muryar wanda ya dauki bidoyon yana ce:

"Mun yi mamaki matuka, yadda yake cin abinci da yaron da bai sani ba, ya yi amfani da cokalin da yake cin abincin yana ciyar da yaron.
"Wannan abu ya yi mana dadi sosai, idan har ana maganar kyakkyawar zamantakewa, to irin wannan yanayin nake magana akai."

Kalli bidiyon da ke ƙasa wanda @Imranmuhdz ya wallafa:

Kara karanta wannan

Rana ta ɓaci: Mutane sun kashe wani ɓarawo yana ƙoƙarin satar babur a masallaci

Ana kallon lokacin Ramadan a matsayin wani wata na sadaka da sada zumunci, da kuma bayar da tallafi musamman ga masu bukata.

A wannan lokacin, Musulmi suna karkatar da hankulansu wajen zurfafa a yawan ibada da neman gafarar zunubansu tare da neman shiga aljanna bayan sun mutu.

Ra'ayoyin mutane game da wannan bidiyo

@paul_khalifa_II ya ce:

"Meyasa dole sai ka yi amfani da addini don tallata kai?
"Kai ba musulmi ba ne, me zai hana ka goyi bayan wasu addinai kuma ka girmama su
"Ba ka buƙatar shiga cikin ayyukansu don yin hakan."

@sir_dagachi ya tambaya:

"Shin musulmi ne?"

@Nurdincantoma ya ba @sir_dagachi amsa da cewa:

"Dole ne sai kan Musulmi za ka iya yin buda baki da musulmi? Wani irin karimci ne kawai ya nuna."

@AzeezOseni4 ya ce:

"Peter Obi ya fara yakin zabensa na 2027. Tun yanzu ya fara neman jama'a, za mu zuba ido mu gani."

Kara karanta wannan

A madadin yi wa budurwa 'Ramadan Basket', matashi ya sa mahaifiyarsa kukan daɗi

@Fifa737 ya ce:

"Don Allah kowa ya bar shi ya yi abin da yake so mana."

Peter Obi ya ba masallatai kyautar kudi

Ba tun yanzu Peter Obi ya fara ziyartar masallatai ba, ko a shekarar da ta gabata, Legit Hausa ta ruwaito yadda dan siyasar ya rabawa masallatai kudi a lokutan bukin babbar Sallah.

Peter Obi wanda ya kai ziyara wasu masallatai a Awka da Onitsha, ya ba shugabannin Musulmi na yankin cak na kudi domin gyara masallatai biyu da ke a garuruwan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.