A Karo Na Biyu, Gwamnan Arewa Ya Fara Raba Tallafin Kudi da Abinci Na N11.4bn a Jiharsa
- Gwamnan Kaduna ya kaddamar da fara rabon kayan tallafi karo na biyu ga mazauna jihar domin cika umarnin shugaban ƙasa
- Malam Uba Sani ya ce a wannna karon gwamnati za ta raba tireloli 128 na shinkafa da masara ga talakawa, gajiyayyu da marasa galihu
- Ya kuma bayyana irin gwaggwaɓan tanadin da aka yi wa masu kanana da matsakaitan sana'o'i a faɗin Kaduna
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Gwamna Uba Sani ya kaddamar da rabon tallafi kashi na biyu a wani kwarya-kwaryar biki aka shirya a jihar Kaduna ranar Litinin.
Wannan na ɗaya daga cikin matakan da gwamnan ya ɗauka domin rage raɗaɗin wahalar rayuwa da ake ciki bisa umarnin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Da yake jawabi a wajen kaddamar da rabon tallafin karo na biyu ga ‘yan jihar, Gwamna Sani ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna za ta kashe Naira Biliyan 11.4 a wannan karon.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sanarwan da ya wallafa a shafinsa na manhajar X, gwamnan ya ce za su ci gaba da kokarin rage raɗaɗi ga talakawa da marasa galihu a faɗin jihar.
Ya ce:
"Yau za mu fara rabon tireloli 128 na shinkafa da masara na N3.4bn ga talakawa, marasa karfi da marasa galihu a Kaduna, muna sa ran aƙalla mutum miliyan ɗaya za su amfana."
Gwamna Sani ya fara raba tallafin N50,000
Uba Sani ya kuma sanar da cewa gwamnatinsa ta fara tura tallafi ga ƙanana da matsakaitan ƴan kasuwa 7,800, waɗanda ke samun tallafi daga N100,000 zuwa N1m, kudin ya danganta da girman sana'a.
Ya ƙara da cewa an ware N4.2bn domin raba tallafin tsabar kudi, takin gona da kayan noma ga talakawa, masu kananan sana'o'i, naƙasassu, ƴan gudun hijira, marayu, mata da matasa.
Gwamnan ya ci gaba da cewa magidanta, talakawa da marasa galihu 9,800 ciki har da naƙasassu sama da 1,000 sun fara karbar tallafin kudi Naira 50,000 kowanensu.
Ya gargadi masu shirin sacewa ko karkatar da kayan su canza tunani, inda ya ce ya yi tanadin tsauraran matakan tsaro domin kare motocin da ke kai shinkafa da masara zuwa wurare daban-daban.
Mamban APC a Unguwar Mu'azu, karamar hukumar Kaduna ta Kudu ya shaida wa Legit Hausa cewa wannan tallafin ya leka kusan gidan kowa tun a kashin farko.
Aliyu Zaharaddeen ya ce Uba Sani ya ɗauko hanyar tsamo mutane da yawa daga halin ƙunci idan har waɗanda suka ci gajiyar shirin za su yi amfani da tallafin yadda ya dace.
A kalamansa ya ce:
"Ni kaina kanwata ta samu, ai wannan tallafi zan iya ce maka ya leka kusan kowane gida, idan kai baka samu ba to wani a danginku ya samu."
"Idan ka duba jawabin gwamna a wurin kaddamar da kashi na biyu, tallafin masu sana'o'in nan zai taka rawa wajen tsamo mutane daga wahala, muna fatan su yi amfani da kuɗin yadda ya dace."
Ramadan: Buni ya fitar da N100 na ciyarwa
A wani rahoton kuma Mai Mala Buni ya amince da fitar da kuɗi Naira miliyan 100 domin ciyar da marasa galihu kowace rana a watan Ramadan.
Kwamishinan addinai na jihar Yobe, Yusuf Umar, ne ya tabbatar da haka yayin da yake duba aikin raba kayan abinci ga masu girki da ƴan kwangila.
Asali: Legit.ng