Shugabannin APC Sun Faɗawa Tinubu Mataki 1 da Ya Kamata Ya Dauka Kan Wasu Hafsoshin Tsaro a Najeriya

Shugabannin APC Sun Faɗawa Tinubu Mataki 1 da Ya Kamata Ya Dauka Kan Wasu Hafsoshin Tsaro a Najeriya

  • Jagororin jam'iyyar APC mai mulki sun roƙi shugaban ƙasa, Bola Ahned Tinubu ya kori duk wani shugaban tsaro da ya gaza aikin da ake buƙata
  • Ƙungiyar shugabannin APC na jihohi ce ta bayyana haka yayin ganawa da Shugaba Tinubu a Villa da ke birnin tarayya Abuja
  • Alphonsus Eba, sakataren ƙungiyar ya ce lokaci ya yi da za a riƙa tuhumar kowane hafsan tsaro ya yi bayanin abin da ya aikata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ƙungiyar shugabannin All Progressive Congress (APC) ta roki shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya kori duk wani hafsan tsaron da ya gaza aikin da ke tsammani.

Sakataren ƙungiyar, Alphonsus Oga Eba, ne ya faɗi haka sakamakon karuwar hare-haren garkuwa da mutane da sauran matsalolin tsaron da suka addabi ƙasar nan.

Kara karanta wannan

Iftaar: Abin da Shugaba Tinubu ya faɗawa gwamnoni a wurin buɗe bakin azumin Ramadan a Villa

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Shugabannin APC na jihohi sun gana da Tinubu a Villa Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ya yi wannan furucin ne yayin hira da masu ɗauko rahoto a gidan gwamnati jim kaɗan bayan ganawa da Shugaba Tinubu a fadar shugaban kasa ranar Jumu'a, 15 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro, shugaban jam'iyyar APC reshen jihar Kuros Riba, Mista Eba ya ce:

"Duk inda aka samu wani ɗan sanda, kwamishinan ƴan sanda ko wani jami'in tsaro na kowace hukumar tsaro yana wasa da aikinsa, ya kamata shugaban ƙasa ya buga masa sandar kora.

Mista Eba ya yabawa Bola Tinubu bisa goyon bayan da yake baiwa hukumomin tsaro da ware musu maƙudan kuɗi a kokarin magance garkuwa da mutane da sauran muyagun laifuka.

Wace shawara shugabannin APC suka ba Tinubu?

A rahoton Punch, yayin da yake jawabi kan abin da suka tattauna da Tinubu a taron, Eba ya ci gaba da cewa:

Kara karanta wannan

"Har yanzu ni mamban jam'iyyar PDP ne" Ministan Tinubu ya yi magana kan sauya sheƙa zuwa APC

"Mun zo ne tare da shawara ɗaya da muke son isar da ita ga shugaban kasa, babu wani ɗan kasa da yake tunanin shugaban kasa, babban kwamandan askarawan Najeriya zai ɗauki makamai ya tafi filin yaƙi.
"Wannan dalili ne ya sa yake da muƙarrabai a hukumomin tsaro daban-daban, amma abin da muka faɗawa shugaban kasa, ta hanyar ba da shawara shi ne lokaci ya yi da za a tuhumi mutane kan abinda suka aikata."

Ramadan: Abin da Tinubu ya faɗa wa gwamnoni

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci gwamnoni su jingine siyasa kana su haɗa kai da gwamnatin tarayya domin gina ƙasar nan

Shugaban ƙasa ya bayyana haka ne a wurin buɗe baki 'Iftaar' na azumin Ramadan a fadarsa da ke Abuja ranar Alhamis.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262