Gwamna Uba Sani Ya Tona Asirin Inda Aka Kai Daliban da Aka Sace a Kaduna, Bayanai Sun Fito
- Gwanna Uba Sani na jihar Kaduna ya bayyana gaskiya inda aka kai daliban makaranta da aka sace 285 a jihar Kaduna
- Uba Sani ya ce a yanzu haka yaran ba su cikin jiharsa inda ya ce an tafi da su jihohin da ke makwabtaka da Kaduna
- Gwamnan ya bayyana haka ne bayan shan ruwa da Shugaba Tinubu a fadarsa a daren jiya Alhamis 14 ga watan Maris
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Yayin da ake ƙoƙarin ceto daliban makaranta 285 da aka sace a jihar Kaduna, an gano inda aka kai su.
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna ya bayyana cewa an dauki yaran zuwa jihohi makwabta, cewar Arise TV.
Menene Uba Sani ya fada kan sace daliban?
Gwamna ya bayyana haka yayin hira da 'yan jaridu a fadar shugaban kasa bayan shan ruwa tare da Shugaba Bola Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sani ya bada kwarin gwiwar cewa za a ceto yaran nan ba da jimawa ba da hadin kan jami'an tsaro.
"Mun yi ganawa da masu ruwa da tsarki a harkar tsaro domin ganin an kawo karshen matsalar ba iya jihar Kaduna ba."
"Mun tattauna abubuwa masu muhimmanci inda muka bukaci yin amfani da tsarin yanki wurin dakile matsalar, mun fahimci yaran da ka sace an wuce da su jihohi makwabta"
- Uba Sani
Ya sha alwashin kawo karshen rashin tsaro
Har ila yau, ya tabbatar da himmatuwar gwamnoni yankin domin inganta tsaro da kuma kawo karshen matsalolin da ta ke fama da su.
Wannan na zuwa ne bayan sace daliban firamare 285 a makaranta da ke Kurigi a jihar Kaduna.
Sace daliban ya jawo kace-nace tare da kira da Gwamnatin Tarayya da ta kara kaimi wurin kare rayukan mutanen a kasar.
Har ila yau, Sheikh Ahmed Gumi ya bukaci yin sulhu da 'yan bindiga domin ceto daliban da kuma sauran wadanda aka sace.
Rashin tsaro: Gwamnoni sun hadu da Ribadu
A baya, mun ruwaito muku cewa gwamnonin Arewacin Najeriya 19 sun yi wata ganawa da mai ba Shugaba Tinubu shawara a ɓangaren tsaro, Nuhu Ribadu.
Yayin ganawar, gwamnonin sun nuna rashin jin dadinsu ganin yadda ake ta amfani da tsari daya wurin dakile matsalar tsaro a yankin.
Asali: Legit.ng