Aikin Rusau: Gwamnan PDP Ya Rushe Ƙauyuka 12 da Gidaje 500? Gaskiya Ta Bayyana

Aikin Rusau: Gwamnan PDP Ya Rushe Ƙauyuka 12 da Gidaje 500? Gaskiya Ta Bayyana

  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya fara rusau a Ibadan, babban birnin jihar inda aka fara zargin ya rushe gidaje masu ɗinbin yawa
  • Rahoto ya nuna rusau zai shafi kauyuka 12 da ke kusa da titin Circular a ƙaramar hukumar Ona Ara ta jihar, amma wani shugaban al'umma ya koka
  • Kwamishinan filaye, gidaje da raya karkara na jihar Oyo, Williams Akinfunmilayo, ya ce gidaje 50 aka rushe amma duk wanda ke da takardu ya je ya karɓi diyya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ibadan, jihar Oyo - Gwamnatin jihar Oyo ƙarƙashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde ta fara rusau na gidaje masu ɗumbin yawa a Ibadan, babban birnin jihar.

Kara karanta wannan

"Har yanzu ni mamban jam'iyyar PDP ne" Ministan Tinubu ya yi magana kan sauya sheƙa zuwa APC

An fara rusau ne a kauyen Fashade ranar Talata, 12 ga watan Maris, 2024 a kusa da titin Circular kuma ana tsammanin zai taɓa kauyuka 12 a ƙaramar hukumar Ona-Ara.

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo.
Gwamnatin Oyo ta fara rusau a Ibadan Hoto: Seyi Makinde
Asali: Twitter

Da yake jawabi kan wuraren da rusau ɗin ya shafa, Abdulfatal Amubikan, shugaban al'umma a ɗaya daga cikin yankunan ya koka kan yawan gidajen da aka rushe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amubikan ya shaida wa jaridar Punch ranar Laraba, 12 ga watan Maris cewa "an rushe gidaje kusan 500."

Gwamnatin Oyo ta fayyace gaskiyar rushe-rushe

Da yake mayar da martani ta wayar tarho, Williams Akinfunmilayo, kwamishinan filaye, gidaje da raya karkara ya tabbatar da fara rusau a Ibadan.

Ya bayyana cewa wannan rusau da aka fara zai shafi duk wasu gine-gine da aka yi kusa da titin Circular.

A rahoton News Nigeria, kwamishinan ya ce:

Kara karanta wannan

Bayan kalaman Tinubu, gwamnan Arewa ya ƙara wa ma'aikata albashi a watan azumin Ramadan

"Yanzu ba daɗewa na tuntubi tawagar da ke aikin kuma sun faɗa mun cewa bai fi gine-gine 50 suka taɓa ba, amma har mutane sun fara cire rodi tun kafin su isa wurin.
"Ba wanda ya rushe gidaje 500 kuma waɗanda ma muka rushe sune waɗanda ba su wuce mita 100 zuwa 150 tsakaninsu da titin Circular ba."

Gwamna Makinde zai biya diyyar rushe-rushe?

Akinfunmilayo ya kuma kara da cewa gwamnatin Makinde za ta biya diyya ga duk wani mai gida da yake da takardar mallaka ta gaskiya sannan ya bukaci su zo sakatariya da takardunsu.

Ya bayyana cewa gwamnati ta karɓi kusan mita 500 na gefen titin a hagu da dama. Don haka a shirye take ta biya duk wanda yake da takardu na gaskiya diyya.

Kungiyar BudgIT ta goyi bayan Abdul Ningi

A wani rahoton kuma sababbin bayanai na kara fitowa kan cushe a kasafin kuɗin 2024 yayin da ƙungiyar BudgIT ta tabbatar da zargin Sanata Abdul Ningi.

Sanata Ningi mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya ya yi zargin cewa akwai wasu kuɗi N3.7trn da aka cusa a kasafin waɗanda babu bayani a kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262