"Na Karbi N266m": Abaribe, Ndume Sun Magantu Kan Ikirarin Ningi Na Cushe a Kasafin 2024

"Na Karbi N266m": Abaribe, Ndume Sun Magantu Kan Ikirarin Ningi Na Cushe a Kasafin 2024

  • Sanatoci biyu a Najeriya sun yi martani kan ikirarin da Sanata Abdul Ningi da aka dakatar ya yi na cewa an yi cushe a kasafin 2024
  • Sanata Enyinnaya Harcourt Abaribe ya ce ya samu N266m daga kudin yayin da Ali Ndume ya yi ikirarin cewa ya samu fiye da N200m
  • Hakan ya biyo bayan zargin da aka yi wa Ningi na cewa ya furta kalaman karya da tayar da tarzoma a majalisar dattawan kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

FCT, Abuja - Sanata mai wakiltar Abia ta Kudu, Enyinnaya Harcourt Abaribe, ya ce shi sam bai karbi N500m da ake ikirarin manyan sanatoci sun samu daga cikin kasafin kudin 2024 ba.

Kara karanta wannan

Cushe a kasafin 2024: PDP ta bukaci Akpabio ya yi murabus, an samu karin bayani

Abaribe wanda ya bayyana hakan a ranar Laraba, 13 ga watan Maris, ya ce Naira miliyan 266 kacal ya samu daga kudin.

Sanata Ndume da Abaribe sun magantu kan cushe a kasafin kudi
Sanata Ndume da Abaribe sun yi magana a kan karbar N500m daga kasafin 2024.Hoto: Sen. Muhammad Ali Ndume, Sen Abaribe Harcourt Enyinnaya
Asali: Facebook

Abaribe ya ce ya samu N266m

Wani dan majalisar dattawa mai wakiltar Kuros Riba ta Arewa, Sanata Jarigbe Agom-Jarigbe, ya yi ikirarin cewa manyan sanatoci sun karbi N500m daga cikin kasafin kudin shekarar 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya biyo bayan cece-kuce da ake ta yi kan zargin an yi cushen kudi da Sanata Abdul Ningi ya yi a wata hira da 'yan jarida.

Da yake mayar da martani kan lamarin, Sanata Abaribe ya ce Ningi ya san kuskure ne fadar maganar da ba zai iya kare kansa ba, domin shi ba sabon dan majalisar dattawa ba ne, inji rahoton Daily Trust.

Abaribe ya kara da cewa, duk da cewa shi kansa babban sanata ne a majalisar, sai dai bai karbi N500m da Jarigbe yake ikirari ba.

Kara karanta wannan

Abdul Ningi: Gwamnan PDP a Arewa ya nuna goyon bayansa ga sanata, ya fadi matakin da zai dauka

Ndume ya ce ya samu sama da N200m

A nasa martanin, Sanata Ali Ndume, ya ce a matsayinsa na babban jami’i a majalisar dattawa ta goma, ya samu sama da N200m don gudanar da ayyukan mazaba daga kasafin kudin.

Sanatan mai wakiltar Borno ta Kudu ya bayyana haka ne a shirin siyasa na gidan talabijin na Channels a ranar Laraba, inda ya ce:

"Abokan aiki na sun san cewa na fi su samun kudin saboda su ba su da mukami irin nawa."

Da aka tambaye shi ko maganar da Agom-Jarigbe ya yi gaskiya ne, Ndume ya ce:

"Bambanci ne da ya ke a fili, ba daya muke ba; dukkan dabbobi daidai suke amma dole za ka samu wasu sun fi wasu. Abin da ya faru ke nan, kuma kowa ya amince da hakan."

Gwamnan Bauchi ya goyi bayan Ningi

A wani labarin, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya tabbatar da goyon bayan gwamnatin jihar ga Sanata Abdul Ningi biyo bayan dakatarwar da majalisar dattawa ta yi masa na tsawon watanni uku.

Kara karanta wannan

Ningi: Jerin sanatocin Najeriya da aka dakatar daga 1999 zuwa 2024 da kuma dalilin da ya sa

Sanata Ningi mai wakiltar mazabar Bauchi ta tsakiya ya fuskanci dakatarwar ne biyo bayan furucin da ya yi game da yadda aka yi cushen Naira tiriliyan 3.7 a kasafin kudin 2024.

Daga bisani Sanata Ningi ya ajiye mukaminsa na shugaban kungiyar Sanatocin Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.