Tinubu Ya Yi Wani Sabon Nadi Mai Muhimmanci, Ya Maye Gurbin Wanda Buhari Ya Nada

Tinubu Ya Yi Wani Sabon Nadi Mai Muhimmanci, Ya Maye Gurbin Wanda Buhari Ya Nada

  • Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin tsohon kwamishina a jihar Legas, Dayo Mobereola a matsayin sabon shugaban hukumar NIMASA
  • Naɗin Mobereola ya biyo bayan murabus ɗin Bashir Jamoh wanda tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa kan muƙamin
  • Sabon shugaban hukumar ya yi aiki a ƙarƙashin Tinubu lokacin yana gwamnan jihar Legas a matsayin shugaban hukumar LAMATA, muƙamin da ya riƙe na tsawon shekaru takwas

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya sanar da naɗin Dayo Mobereola a matsayin sabon darakta-janar na hukumar kula da harkokin ruwa ta Najeriya (NIMASA) na tsawon shekara huɗu.

Nadin Mobereola ya biyo bayan tafiyar Bashir Jamoh, wanda tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa a ranar 4 ga watan Maris, 2020.

Kara karanta wannan

Batun ba dalibai rance ya bi ruwa: Gwamnatin Tinubu ta dakatar da shirin aron kudin karatu

Tinubu ya nada sabon shugaban hukumar NIMASA
Shugaba Tinubu ya maye gurbin wanda Buhari ya nada shugaban hukumar NIMASA Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Muhammadu Buhari
Asali: Twitter

NIMASA tayi sabon shugaba a Najeriya

An bayyana naɗin Mobereola ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaba Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Ajuri Ngelale, ya fitar a ranar Talata, 12 ga watan Maris.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin Shugaba Tinubu kan kafafen sadarwa na zamani, Dada Olusegun, ya sanya sanarwar naɗin Mobereola a shafinsa na X.

Wanene sabon shugaban hukumar NIMASA?

Sabon shugaban hukumar ta NIMASA ya taɓa yin aiki a ƙarƙashin Tinubu lokacin da yake gwamnan jihar Legas a matsayin manajan darakta na hukumar kula da sufuri ta Legas (LAMATA) daga shekarar 2003 zuwa 2015.

Ya kuma riƙe muƙamin kwamishinan sufuri na jihar daga shekarar 2015 zuwa 2016.

Ya samu gogewa sosai wajen aiki da kamfanoni masu zaman kansu, ciki har da kamfanin AFM Consulting Plc da ke Landan, inda ya riƙe mataimakin manajan darakta.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya naɗa tsohon shugaban PDP da wasu mutum 2 a manyan muƙamai

Shugaba Tinubu ya sa labule da Akpabio

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya gana da shugabannin majalisar dattawa ƙarƙashin jagorancin Sanata Godswill Akpabio.

Ganawar ta su na zuwa ne biyon bayan dakatarwar da majalisar ta yi wa Sanata Abdul Ningi, kan zargin da ya yi na cewa an yi cushen N3.7tr a kasafin kuɗin shekarar 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng