Yan Bindiga Sun Kai Sabon Hari Kaduna, Sun Yi Awon Gaba da Mutane da Dama
- 'Yan bindiga sun yi awon gaba da mutane akalla 61 a wani sabon hari da suka kai garin Buda da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna
- Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigar sun kai harin a daren Litinin inda suka tafi da maza, mata da kananan yara, har da mai shayarwa
- Wani mazaunin garin, Lawal Abdullahi ya ce tun bayan tafiyar wani kwamandan sojoji da aka fi sani da (Tega) 'yan bindiga suka addabe su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Kajuru, jihar Kaduna - Akalla mutane 61 ne wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a wani farmaki da suka kai garin Buda da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
Jaridar Vanguard ta ruwaito wani daga cikin wadanda suka tsira daga harin ya ce 'yan bindigar sun yi awon gaba da maza, mata da yara, har da wata mata mai shayarwa.
Yan bindigar sun bude wuta kan kowa
“Al’amarin ya yi muni sosai, har yanzu ba mu ji duriyarsu ba tun bayan tafiya da su a ranar Litinin. Muna kira ga gwamnati da ta dauki matakin gaggawa.":
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
- A cewar sa.
The Cable ta tattaro cewa har yanzu babu wani martani daga 'yan sanda kan faruwar kai farmakin.
Sai dai Dauda Kajuru, wani mazaunin garin ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun yi harbi kan mai uwa da wabi yayin farmakin.
Hare-hare bayan tafiyar kwamandan sojoji
Ya kuma yi kira ga hukumomi da su tura karin jami’an tsaro a yankin, yana mai cewa:
"Yan uwana na cikin wadanda aka sace kuma bisa ga bayanin muka samu, 'yan bindigar da wadanda suka sace ba su kai ga isa inda suke so ba, don haka za a iya cimma su cikin gaggawa."
Wani dan garin Buda, Lawal Abdullahi wanda shi ma ya tsallake rijiya da baya amma matarsa na cikin wadanda abin ya shafa, ya kuma tabbatar da cewa mutane 61 aka tafi da su.
Ya yi nuni da cewa tun bayan sauke wani kwamandan sojoji da aka fi sani da (Tega) ‘yan bindiga suka dawo da kai farmaki kauyukan ba kakkautawa.
Dalibai 287 aka sace a Kaduna - Abdullahi
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta tattaro cewa dalibai 287 ne 'yan bindiga suka sace a makarantar firamare da sakandare ta garin Kuriga da ke jihar Kaduna.
Sani Abdullahi, shugaban makarantar da aka dauke daliban ya shaida wa gwamnan jihar, Uba Sani cewa shima da kyar ya sha a hannun 'yan bindigar tare da wasu dalibai.
Asali: Legit.ng