Yan Bindiga Sun Kai Farmaki Asibitin Jami'ar Tarayya, Sun Tafka Mummunar Ɓarna a Watan Azumi
- Ƴan bindiga sun kai farmaki asibitin koyarwa na jami'ar tarayya ta UNTH a jihar Enugu da ke Kudu maso gabashin Najeriya
- Wasu majiyoyi daga asibitin sun bayyana cewa maharan sun yi awon gaba da mataimakiyar darakta da kuma jami'in tsaro ɗaya
- Rundunar ƴan sanda da hukumar gudanarwan asibitin ba su ce komai ba amma wani ma'aikaci ya koka kan halin da suka shiga
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Enugu - Wasu ƴan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai farmaki asibitin koyarwa na jami'ar Najeriya (UNTH) da ke Ituku Ozalla a jihar Enugu.
Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kutsa kai cikin asibitin ne da safiyar yau Talata, 12 ga watan Maris, 2024, jaridar Vanguard ta ruwaito.
‘Yan bindigar sun kuma yi awon gaba da wata mace mataimakiyar daraktar sashen jinya da wani jami’in tsaro da ke aiki a asibitin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda maharan suka shiga harabar asibitin UNTH
An tattaro cewa maharan sun biyo sawun mataimakiyar daraktan da ke cikin motar SUV har zuwa harabar asibitin da misalin ƙarfe 9:00 na safiya.
Majiyoyi a asibitin sun shaida wa wakilin jaridar The Nation cewa ‘yan bindigar sun harbi motar matar kai tsaye, wanda hakan ya tilasta mata tsayawa kafin daga bisani su tafi da ita.
An ga motar da mataimakiyar daraktan ke ciki a ajiye gefe guda a wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, harsashi ya fasa gilashin gefen fasinja.
Wane mataki mahukunta suka ɗauka?
Har kawo yanzu, rundunar ƴan sanda na reshen jihar Enugu da hukumar gudanarwar asibitin ba su tabbatar da aukuwar lamarin ba.
Daya daga cikin majiyoyin ya ce lamarin ya faru ne a daidai wurin da aka yi garkuwa da wani likita a ƴan makonnin da suka gabata.
“Wannan abin bakin ciki ne, mun rasa zaman lafiya kwata-kwata a wannan asibitin, ko ina sai tashin hankali,” in ji wani ma’aikacin asibitin da ya nuna damuwa.
Yan bindiga sun nemi fansar N40trn
A wani rahoton kuma Ƴan bindiga sun nemi a haɗa masu Naira tiriliyan 40 a matsayin kuɗin fansar mutum 16 da suka yi garkuwa da su a jihar Kaduna
Maharan sun sace waɗannan mutanen ne daga kauyen Gonin Gora da ke ƙaramar hukumar Chikun ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu, 2024
Asali: Legit.ng