Tinubu Ya Tura Kasafin Kuɗin FCTA Na 2024 Zuwa Majalisa a Watan Azumi, Bayanai Sun Fito

Tinubu Ya Tura Kasafin Kuɗin FCTA Na 2024 Zuwa Majalisa a Watan Azumi, Bayanai Sun Fito

  • Bola Ahmed Tinubu ya aike da kasafin kuɗin 2024 na hukumar gudanarwa ta Abuja (FCTA) ga majalisar wakilan tarayya
  • Shugaban ƙasar ya buƙaci majalisar ta hanzarta aiki kan kasafin kuma ta amince da shi, hakan na kunshe a wasiƙar da ya tura majalisar ranar Talata
  • Majalisar ta miƙa sakon shugaban ƙasar ga kwamitin kasafin kuɗin domin muhawara a kansa gabanin amincewa da shi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya aike da ƙiyasin kasafin kuɗin hukumar gudanarwa ta babban birnin tarayya Abuja (FCTA) ga majalisar wakilai ta ƙasa.

Shugaba Tinubu ya tura kundin kasafin kuɗin FCTA na shekarar 2024 ga majalisar wakilan tarayya a ranar Talata, 12 ga watan Maris, 2024.

Kara karanta wannan

Ningi: Majalisa ta dauki mataki kan Sanatan da yayi zargin cushen N3tr a Kasafin 2024

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
An yi kasafin kuɗin 2024 na FCTA Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Me kasafin kuɗin FCTA 2024 ya ƙunsa?

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, wasiƙar da shugaban ƙasar ya aika majalisar ba ta bayyana adadin yawan kuɗin da kasafin ya ƙunsa ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasiƙar ta ce:

"Duba da sashi na 121 da 299 na kundin tsarin mulkin ƙasar nan na 1999, ministan Abuja ya shirya kasafin kuɗin 2024 na FCT wanda ke gaban majalisa yanzu domin amincewa.
"An tsara kasafin kuɗin ne bisa yawan kuɗin shigar FCTA da kuma lura da tsarin bunƙasa kasafin kuɗin tarayya da ajendar sabunta fata.
"FCTA tana ba da fifiko a ɓangarorin inganta kiwon lafiya, samar da ayyukan yi, ƙarfafa matasa da haɓaka aikin noma da nufin tsamo mutane da dama daga kangin talauci.
"Bisa haka nake gabatar da kasafin kudin 2024 na FCTA kuma na yi imanin cewa zai samu kyakkyawar kulawa da amincewar majalisar wakilai cikin gaggawa."

Kara karanta wannan

"Ka da ka zama kamar Buhari": An ba Tinubu shawarar magance matsalar rashin tsaroS

Majalisa ta ɗauki mataki kan kasafin FCTA?

Majalisar ta kuma mika sakon Shugaba Tinubu ga kwamitin kasafin kuɗi domin yin aikin da ya dace gabanin ta amince, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ta kace-nace kan kasafin kuɗin 2024 wanda majalisun tarayya suka aminta da shi.

Hakan ya biyo bayan kalaman da aka jinginawa Sanata Abdul Ningi cewa akwai wasu kudi N3trn da aka amince da su kuma ba su cikin kasafin kuɗin 2024.

Atiku ya fara shirin kafa sabuwar jam'iyya

A wani rahoton, an ji tsohon mataimakin shugaban ƙasa da wasu manyan ƙusoshin APC sun fara shirin kafa sabuwar jam'iyyar siyasa.

Atiku, tsohon gwamnan Zamfara da Abdul Ningi suna cikin tawagar da mai yiwuwa za su yi kokarin maimaita abinda ya faru a 2013.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262