Kiristar Budurwa Ta Fadi Natsuwar Da Take Samu a Karatun Kur'ani

Kiristar Budurwa Ta Fadi Natsuwar Da Take Samu a Karatun Kur'ani

  • Wata budurwa Kirista ta yi tsokaci kan halin da ta kan shiga a duk lokacin da take sauraron karatun littafin Kur'ani
  • Duk da kasancewarta Kirista, Rebecca ta ce ta kan samu nutsuwa sosai a duk lokacin da aka saka karatun Kur'ani a inda take
  • Ta ce lallai ba sai mutum ya kasance Musulmi bane kawai zai fahimci akwai wani abu na musamman game da littafin mai tsarki

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wata matashiyar budurwa ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta bayyana yadda ta kan ji a duk lokacin da wani ke karanta Al-Kur'ani.

Matashiyar mai suna Rebecca wanda ba Musulma ba ce, ta ce ta kan ji dadin sautin da ke fita na Al'Kur'ani a duk lokacin da wani ke karanta shi.

Kara karanta wannan

Kotu ta haramtawa magidanci magana da matarsa na tsawon kwana da kwanaki

Budurwa kirista ta fadi nutsuwar da ke tattare da Kur'ani
Kiristar Budurwa Ta Fadi Natsuwar Da Take Samu a Karatun Kur'ani Hoto: Wikipedia
Asali: UGC

A cewarta, wani abokin aikinta wanda yake Musulmi ya sa karatun kira'a inda ita kuma ta dunga jin wani abu game da hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wata wallafa da ta yi a shafinta na X, Rebecca ta kuma jaddada cewar ba dole sai mutum ya kasance Musulmi bane zai ji wani dadi da nutsuwa a duk lokacin da ake karatun littafin mai tsarki.

"Ni ba Musulmba ba ce amma na kan ji dadin sautin Kur'ani a duk lokacin da wani ke karanta sa,
wani abokin aikina Musulmi ya saka kira'a a yau sannan na rika jin wani yanayi.
"Ina ganin akwai wani abin game da Kur'ani da ba sai mutum ya kasance Musulmi ba kafin ya ji wani nutsuwa a duk lokacin da aka saka shi."

- Rebecca

Ga wallafar tata a kasa:

Kara karanta wannan

Budurwa ta ce tana samun N4m duk wata daga man ja, bidiyon ya girgiza intanet

Jama'a sun yi martani kan furucin Rebecca

Mutane da dama sun yi martani tare da yiwa Rebecca sha'awar shiga Musulunci. Legit Hausa ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

@Itz_zayyad1 ya yi martani:

"Kira kenan In sha Allah."

@sir_eeid ya ce:

"Allah ya sa ki musulunta."

@khalid_koiki ya ce:

"Haka yake! Kawai ki furta kalmomin 'yar'uwa."
"Karbi Shahada ☺."

@AhmadBYusuf3 ya ce:

"Masha Allah Allah ya yi maki jagora zuwa addinin Musulunci."

@Ameesh__ ta ce:

"Allah yasa ki ga haske wata rana."

@tudunwada__mi:

"Kawai ki karbi Musulunci."

@sattitigeress2:

"Ma sha ALLAH "

@LukwagoRajab ya ce:

"Allah ya yi maki jagoranci zuwa hanya madaidaiciya."

@AnantSharma0301 ta ce:

"Maganar gaskiya nima ina son Kur'ani."

Addinin Musulunci ya samu 'karuwa

A wani labarin, Legit Hausa ta kawo a baya cewa budurwa mai shekaru 18 a duniya, ta bar addininta na kiristanci sannan ta karbi musulunci.

Kyakkyawar budurwa mai suna Blessing ta sauya sunanta zuwa 'Khadijah'. Wannan suna ya shahara a musulunci ne saboda matar manzo SAW.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng