Mutanen Dapchia sun bayyana yadda aka sace ‘Yan Makaranta 105
Mun samu rahoto daga Jaridar Daily Trust inda Mutanen Dapchia su ka bayyana yadda aka sace ‘Yan Makarantar Gwamnatin fasaha ta mata sama da 100 kwanakin baya. ’Har yau dai ba a san inda aka kai ‘Yan matan da aka sace ba.
Shugabar Makarantar ‘Yan Makarantar Hajiya Adama Abdulkareem ta bayyanawa Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Yobe cewa abin ya faru ne lokacin su na cikin gida. Bayan shigowan ‘Yan Boko Haram makarantar ne Malamai su ka tsere.
Wani Malamin Makarantar mai suna Malam Auwal ya samu karyewa a cinya lokacin da yake kokarin tserewa da iyalin sa. Malamin yace don dole ya dauki matar sa domin su tsere amma aka harbe sa a kafa amma Allah yayi yana da sauran kwana.
KU KARANTA: Ministar Jonathan ta samu babban matsayi a kasar waje
Wasu Malaman Makarantar dai sun labe ne a cikin Masallaci lokacin da ‘Yan Boko Haram su ka shigo Makarantar. A lokacin ne aka sace 'Dalibai ‘Yan mata da dama. Wadanda su ke nan su kace ana jin ‘Yan Matan su na ihun ‘Mun shiga uku!’
Wani daga cikin Malaman Makarantar mai suna Malam Dadin Kowa ya taimaka wajen tserewa da ‘yan mata sama da 50. ‘Yan Boko Haram din sun sace wasu mata a bakin kofar makarantar bayan sun yi kokarin tserewa bayan abin ya faru.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng