Bayan Rasuwar Fitaccen Sanata, Tsohon Minista Kuma Dattijo a Arewacin Najeriya Ya Rasu

Bayan Rasuwar Fitaccen Sanata, Tsohon Minista Kuma Dattijo a Arewacin Najeriya Ya Rasu

  • Bayan fitaccen sanata a Arewacin Najeriya ya rasu, an sake babban rashi a Najeriya na tsohon ministan lafiya
  • Marigayin Cif Gabriel Aduku ya rasu ne a yau Litinin 11 ga watan Maris a Amurka bayan fama da jinya mai tsawo
  • Marigayin shi ne tsohon shugaban kungiyar Arewa Consultative Forum kafin sauke shi a mukamin a Disambar 2023

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - An shiga jimami bayan rasuwar tsohon minista kuma tsohon shugaban Arewa Consultative Forum (ACF), Cif Gabriel Aduku.

Aduku ya rasu ne a yau Litinin 11 ga watan Maris a kasar Amurka bayan ya sha fama da jinya mai tsayi, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya amince zai raba tallafin abinci ga talakawa sama da miliyan 2 a Ramadan

Tsohon minista a Najeriya kuma dattijo a Arewa ya rasu
Marigayin ya rasu ne a kasar Amurka a yau Litinin. Hoto: Gabriel Aduku.
Asali: Facebook

Wasu mukamai Aduku ya rike kafin rasuwarsa?

Marigayin kafin rasuwarsa ya rike karamin ministan lafiya a Najeriya kafin daga bisani ya bar kujerar kungiyar ACF.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Cif Gabriel ya samu shugabancin kungiyar ACF ne a watan Mayun shekarar 2023 baya sauka daga kujerar da Audu Ogbe ya yi, cewar The Sun.

Daga bisani an sauke Aduku tare da maye gurbinsa da babban lauya a Najeriya, Mamman Osman a watan Disambar 2023 bayan zargin badakalar kudi.

Wanene tsohon minista, Aduku?

An haifi Aduku ne a ranar 3 ga watan Fabrairun shekarar 1944 a garin Anyigba da ke karamar hukumar Dekina a jihar Kogi.

Marigayin ya rike mukamin sarautar gargajiya ta Amana Ogohi a masarautar Igala da ke jihar Kogi a Arewacin Najeriya.

Har ila yau, Aduku ya na daga cikin wadanda suka kirkiri jam'iyyar PDP inda ya samu yabo na musamman kan tsara tambarin jam'iyyar a shekarar 1998.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsohon Sanatan PDP, Sodangi ya rasu a daren farkon watan Ramadan

Tsohon Sanata a Arewa ya rasu

A baya, mun ruwaito maku cewa an tafka babban rashi bayan Sanata Abubakar Danso Sodangi ya rasu ya na da shekaru 70 da haihuwa.

Marigayin wanda ya wakilci Nasarawa ta Yamma fiye da shekaru 12 a Majalisar Dattawa ya rasu ne a jiya Lahadi 10 ga watan Maris.

Sanata Sodangi aka tabbatar da rasuwarsa a daren jiya Lahadi 10 ga watan Maris wanda aka tabbatar ya ba addinin Musulunci gudunmawa sosai lokacin da ya ke raye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.