'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Kasuwa, Sun Kashe Mutane da Dama Ana Murnar Zuwan Ramadan

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Kasuwa, Sun Kashe Mutane da Dama Ana Murnar Zuwan Ramadan

  • Ƴan bindiga sun kai hari kan mutane a kasuwar wani kauye a ƙaramar hukumar Wase da ke jihar Filato ranar Lahadi
  • Wani shugaban matasa, Abdullahi Hussaini, ya bayyana cewa maharan sun isa kasuwar yayin da jama'a ke tsaka da kasuwancinsu
  • Ya ce nan take suka kashe mutum bakwai kana wasu da dama suka samu raunuka, ya nemi a kara turo jami'an tsaro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu tsagerun ƴan bindiga sun kai sabon hari kan jama'a a kasuwar kauyen Zurak Campani, ƙaramar hukumar Wase a jihar Filato.

Bayanai sun nuna cewa ƴan bindigan sun harbe mutum bakwai har lahira yayin da wasu dama suka samu raunuka a harin na ranar Lahadi.

Kara karanta wannan

Sanarwar Sarkin Musulmi: An ga wata a wasu jihohin Najeriya, za a fara azumi ranar Litinin

Gwamna Celeb Mutfwang na jihar Plateau.
An rasa rayuka a harin ƴan bindiga a Filato Hoto: Celeb Mutfwang
Asali: Facebook

Yadda maharan suka ci karensu ba babbaka

Lamarin ya faru ne a ranar da kasuwar ke ci sa'ilin da mafi yawan mutanen garin suka maida hankali wajen harkokin kasuwancinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani shugaban matasa a yankin, Abdullahi Hussaini, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya shaidawa Daily Trust cewa ‘yan bindigar sun isa kasuwar da misalin karfe 2 na rana a ranar Lahadi.

Ya ce daga zuwan maharan suka buɗe wuta kan mutane da ke harkokin kasuwanci, suka kashe mutum bakwai nan take.

"Ƴan bindiga masu yawa a kan babura sun mamaye kasuwa kana suka buɗe wa mutane wuta kan mai uwa da wabi, sun kashe mutum 7 nan take yayin da wasu da yawa suka ji rauni.
"Maharan sun zo sun aikata abin da ransu ke so ba tare da fuskantar wata turjiya ba saboda kwata-kwata mutane ba su yi tsammanin hari ba. Ƴan bindigan sun gudu amma an turo ƴan sanda domin su dawo da doka da oda."

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya ba hukumar Kwastam sabon umarni kan kayan abincin da ta kwace

"Muna kira da a kara turo jami’an tsaro zuwa yankin saboda ba mu san abin da ka iya faruwa ba nan gaba."

- Abdullahi Hussaini.

Yayin da aka tuntuɓi jami'in hulɗa da jama'a na rundunar ƴan sandan jihar Filato, DSP Alabo Alfred, bai amsa tambayoyin da ƴan jarida suka masa kan harin ba, rahoton Naija News.

Jihohi 14 na fuskantar barazanar hare-hare a Najeriya

A wani rahoton kuma Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta bankaɗo wani tuggu na yiwuwar ƴan bindiga su kai hari makarantu a jihohi 14 a Najeriya.

Hajia Halima Iliya, jagorar shirin samar da kuɗaɗen tsaron makarantu a Najeriya ta ce gwamnati na ƙara tsaurara matakan tsaro a jihohin da abin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262