Emefiele Ya Shiga Uku, EFCC Ta Sake Tuhumar Tsohon Gwamnan CBN Kan Dalili 1 Tak, Ta Yi Bayani

Emefiele Ya Shiga Uku, EFCC Ta Sake Tuhumar Tsohon Gwamnan CBN Kan Dalili 1 Tak, Ta Yi Bayani

  • Yayin da ake ci gaba da shari’ar tsohon gwamna CBN, Godwin Emefiele, hukumar EFCC ta sake runtumo wani korafe kan tsohon gwamnan
  • EFCC ta fitar da wata sanarwa a jiya Laraba 29 ga watan Nuwamba inda ta ce dukkan kwangiloli da Emefiele ya bayar sun saba ka’ida
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan kotun ta ba da belin Emefiele har miliyan 300 wanda ya gagara ciki ka’idojin belin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Hukumar Yaki da Cin Hanci (EFCC) ta yi martani kan shari’ar da ke tsakaninta da tsohon gwamnan CBN, Godwin Emefiele.

Idan ba a mantaba an gurfanar da Emefiele a babbar kotun Tarayya a ranar Talata 28 ga watan Nuwamba kan badakalar biliyan 1.2.

Kara karanta wannan

Murna yayin da a karshe FG ta bayyana ranar biyan basukan masu cin gajiyar N-Power, ta fadi dalilai

EFCC ta sake fito da wani sabon tuhuma kan Emefiele
Emefiele ya sake shiga matsala bayan EFCC ta sake bijiro da wata tuhuma. Hoto: EFCC Nigeria.
Asali: Twitter

Nawa kotun ta bayyana na belin Emefiele?

Kotun tun farko ta ba da belin Emefiele har miliyan 300 wanda ya gagara cika ka’idojin belin, Legit ta tattaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Emefiele na ci gaba da zama a kulle a gidan gyaran hali na Kuje da ke birnin Tarayya Abuja.

A jiya Laraba 29 ga watan Nuwamba, hukumar EFCC ta ce dukkan kwangiloli da Emefiele ya bayar sun saba ka’idar ba da kwangila.

Wace tuhuma ake yi kan Emefiele?

Mai kara Oluwole Owoeye ya bayyana wa babbar kotun cewa tsohon gwamnan ya ba da kwagiloli ba bisa ka’ida ba yayin da ya ke gwamnan CBN.

Owoeye shi ne shugaban sakatariyar kwamitin ba da kwangiloli inda ya shaidawa kotun irin rashin bin ka’ida na Emefiele.

Ya ce duk wata kwangila da ta haura naira miliyan 10 daga babban bankin CBN dole sai ta biyo ta hannun kwamitin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun Koli ta yanke hukunci kan dena amfani da tsaffin takardun naira a Najeriya

Kotu ta ba da belin Emefiele

A wani labarin, Babbar kotun Tarayya da ke Abuja ta ba da belin tsohon gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele.

Kotun da ke zamanta a Abuja ta ba da belin ne akan kudi naira miliyan 300 da kuma wadanda za su tsaya masa.

Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da shari'ar Emefiele kan badakalar makudan kudade.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.