Ramadan: Rundunar Ƴan Sanda Ta Aike da Saƙo Mai Muhimmanci Ga Musulmai a Najeriya
- Rundunar ƴan sanda ta aike da saƙon gaisuwa da taya murna ga Musulmin Najeriya yayin da suka fara azumtar watan Ramadan
- Sufetan ƴan sandan na kasa ya jaddada shirin rundunar na tabbatar da tsaro a lungu da saƙon Najeriya a wannan wata mai albarka
- IG ya roƙi musulmai da su ɗauki halayen tausayi, jin ƙai da taimakon juna a watan azumin wanda ke da matuƙar muhimmanci a musulunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Yayin da al'ummar Musulmi a Najeriya suka tashi da azumin watan Ramadan ranar Litinin, rundunar ƴan sanda ya taya su murnar zuwan wannan wata.
Babban sufetan ƴan sanda na kasa, IGP Kayode Egbetokun, ya ƙara jaddada kudirin rundunar na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a sassan ƙasar nan.
IGP Egbetokun ya ba da wannan tabbaci ne yayin da yake taya ɗaukacin al'ummar Musulmi murnar zagayowar watan azumi mai cike da albarka da ni'ima.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda na kasa, ACP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 11 ga watan Maris.
Saƙon ƴan sanda ga musulmin Najeriya
Sanarwar da rundunar ƴan sanda ta wallafa a shafinta na X watau Twitter, ta ce:
"Yayin da watan Ramadan ya shigo, IGP Kayode Egbetokun, ya mika sakon gaisuwa daga rundunar ƴan sandan Najeriya zuwa ga ɗaukacin al'ummar musulman ƙasar nan.
"A wannan wata mai albarka, rundunar ‘yan sandan Najeriya na ƙara jaddada aniyarta na tabbatar da aminci, tsaro da kwanciyar hankalin dukkan ‘yan kasa.
"Rundunar ƴan sanda ta san mahimmancin mutunta ayyukan addini da al'adu da kuma buƙatar haƙuri, fahimta da haɗin kai a tsakanin al'ummarmu daban-daban."
Halayen da ya kamata musulmi ya ɗauka a Ramadan
Shugaban ƴan sandan ya kuma buƙaci al'ummar musulmai su ɗauki ɗabi'o'i da halayen da aka fi so a watan Ramadan kamar tausayi, karamci da kuma yafiya ga juna.
Ya kuma yi kira ga dukkan ƴan Najeriya su hada kai, tallafa wa juna, samar da zaman lafiya, ƙara danƙon zumunci da hadin gwiwa a wannan wata mai alfarma da bayansa.
Sufetan ‘yan sandan ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su marawa kokarin NPF baya na tabbatar da zaman lafiya tun daga farko har zuwa ƙarshen watan Ramadan.
Ramadan: Tinubu ya ja hankalin attajirai
A wani rahoton na daban Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci masu hannu da shuni da su taimaki talakawa musamman a lokacin azumin watan Ramadan.
Shugaba Tinubu ya faɗi hakan ne a wajen rabon tallafin shinkafa da Sanata Abdul'aziz Yari ya ƙaddamar a Kano.
Asali: Legit.ng