Gwamnan PDP Ya Yi Sa'insa da Akpabio a Wurin Jana'izar Herbert Wigwe, Bidiyo Ya Bayyana

Gwamnan PDP Ya Yi Sa'insa da Akpabio a Wurin Jana'izar Herbert Wigwe, Bidiyo Ya Bayyana

  • Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya caccaki gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara a wurin taron jana’izar marigayi Herbert Wigwe
  • Akpabio ya ce idan babu wani abu a gwagwarmayar siyasa, kada Gwamna Fubara ya tsaya yana kokowa da kowa
  • Ya bayyana hakan ne bayan da Fubara ya nuna shakku kan yadda masu rike da mukaman siyasa a ƙasar nan suke yin ko a mutu ko a yi rai wajen neman mulki lokacin jana’izar marigayi Herbert Wigwe

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Isiokpo, jihar Ribas - Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Ribas da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio sun yi sa'insa a yayin bikin jana'izar tsohon shugaban bankin Access, Dr. Herbert Wigwe, matarsa, Doreen Chizoba da ɗansa, Chizzy a garin Isiokpo, jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Wike vs Fubara: Gwamnan Ribas ya fadi abin da ya yi niyya lokacin shirin tsige shi

Akpabio ya caccaki Fubara
Akpabio ya caccaki Gwamna Fubara Hoto: @SimFubaraKSC/@AkpabioSen
Asali: Twitter

A cikin wani faifan bidiyo da wani mai amfani da shafin X (wanda a baya aka fi sani da Twitter) @kc_journalist ya sanya, Gwamna Fubara ya caccaki ƴan siyasa a ƙasar nan kan neman mulki ta hanyar a mutu ko a yi rai.

Fubara ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wannan yana da alaƙa da siyasarmu, menene wannan gwagwarmayar? Kuna so ku kashe, kuna so ku binne, duka menene hakan?

Wane martani Akpabio ya yi wa Gwamna Fubara?

Da yake mayar da martani ga Fubara, shugaban majalisar dattawan ya bayyana yadda aka hana shi tsayawa takarar mataimakin gwamna.

Akapbio ya bayyana cewa:

"Menene ake fafutukar a kansa? Zan amsa maka. Fafutukar... ba maganar siyasa ba ce.
"A shekarar 2006, na so in zama mataimakin gwamna. Mataimakin gwamnan na wancan lokacin ya gayyace ni ya ce min wannan ofishin ba shi da kuɗi.

Kara karanta wannan

Ana ba tsaro a kasa, Akpabio ya fito ya fadi ci gaban da Tinubu ya kawo a bangaren

"Babu komai a cikinsa. Ban san meyasa ka nace sai kawar da ni daga nan ka hau kujerar ba.
"Kawai, sai wata mata da muke tare ta ce masa kada ya jira a tsige shi ya yi murabus kawai tunda babu komai a ciki.
"Sai ya miƙe ya fara naushinta, sai na gaya masa kada ka buge ta, gaskiya take faɗa maka. Babu komai a ofishin shiyasa nake so saboda ya yi maka kaɗan.
"Don haka mai girma Gwamna Fubara, idan babu komai a fafutukar, kada ka yi."

Fubara ya magantu kan shirin tsige shi

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya yi magana kan ƙoƙarin tsige shi da aka yi a baya.

Gwamnan ya bayyana cewa a lokacin da aka shirya masa hakan, da ya yi amfani da dukkanin ikonsa da an samu rikici a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng