Dakarun Sojoji Sun Shiga Daji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda

Dakarun Sojoji Sun Shiga Daji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda

  • Dakarun sojoji suj samu nasarar yin galaba kan ƴan ta'adda a dajin Sambisa da ke jihar Borno ta yankin Arewa maso Gabashin Najeriya
  • A wani farmaki da sojojin suka kai cikin dajin sun sheƙe ƴan ta'adda uku tare da lalata maɓoyarsu da suke amfani wajen ɓoyewa
  • Sojojin sun kuma ƙwato bindigu da rigae ƙunar baƙin wake da ƴan ta'addan suke amfani da su wajen aikata ta'addanci

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Sojojin Najeriya, a ranar Juma’a, sun kashe ƴan ta’adda uku a wani samame da suka kai dajin Sambisa a jihar Borno.

Sojojin sun kuma lalata maboyar ƴan ta’adda a dajin, cewar rahoton jaridar The Punch.

Sojoji sun sheke 'yan ta'adda
Dakarun sojoji sun sheke 'yan ta'adda a Borno Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Dajin Sambisa dai gwamnatin mulkin mallaka ce ta keɓe shi a matsayin wurin ajiyar namun daji amma ya zama tungar ƴan ta'addar Boko Haram da na ISWAP.

Kara karanta wannan

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar mutum 313 da ake zargi da aikata ta'addanci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Duk da ayyukan share fage da sojoji suke yi a dajin, har yanzu ƴan ta'addan na ci gaba da kawo hare-hare daga can.

Wata sanarwa da daraktan hulɗa da jama’a na rundunar sojojin Najeriya, Manjo Janar Onyema Nwachukwu, ya fitar ta tabbatar da sheƙe ƴan ta'addan.

Yadda sojoji suka sheƙe ƴan bindigan

Ya bayyana cewa bayan da sojojin suka lalata sansanin ƴan ta'addan a dajin, sun kuma ƙwato bindiga ƙirar AK-47 guda biyu da rigar ƙunar baƙin wake, rahoton jaridar PM News ya tabbatar.

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

"Dakarun Sojojin Najeriya da aka tura yankin Arewa maso Gabas a ci gaba da kai farmaki ga ƴan ta’adda, sun kai hari a ranar Juma’a 8 ga watan Maris, 2024, inda suka yi nasarar kai farmaki kan sansanin ƴan ta’addan da ke yankin Arra na dajin Sambisa.

Kara karanta wannan

Kisan sojoji a Delta: Abubuwan sani 5 dangane da jana'izar da za a yi wa jami'an tsaron

"A yayin farmakin, sojojin sun yi nasarar halaka ƴan ta'adda uku da suka haɗa da ɗan ƙunar baƙin wake ɗaya tare da lalata maɓoyarsu da ke yankin. Bayan binciken kwakwaf, sojojin sun ƙwato bindigu ƙirar AK-47 guda biyu da rigar ƙunar baƙin wake ɗaya."

Onyema ya kuma ce a wani samame da aka kai a karamar hukumar Kukawa da ke Borno, an kashe ɗan ta’adda guda ɗaya tare da lalata matsugunin su.

Dakarun sojoji sun yi raga-raga da ƴan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa hedikwatar tsaro ta ƙasa (DHQ) ta bayyana cewa dakarun sojoji da ke aikin cikin gida a fadin kasar nan sun kashe 'yan ta'adda 210 a mako ɗaya.

Bayan haka kuma sojojin sun kama ƴan ta'adda 142 kana suka ceto mutane 46 da aka yi garkuwa da su cikin mako ɗaya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng