Budurwa Ta Siya Katon Gida a Turai Tana da Shekaru 22, Ta Yi Murnar Zama Mai Gidan Kanta
- Wata mata da ta cimma abubuwan da mutane da dama ke mafarkin mallaka a ganiyar kuruciya ta yi bidiyo a dandalin TikTok
- Matashiyar ta tsaya a gaban sabon gidanta sannan ta bayyana cewa ta kafa tarihi ta hanyar zama mai gidan kanta
- Mutane sun bayyana cewa labarinta ya karfafa masu gwiwa, kuma suna fatan ginawa ko siyawa kansu gida nan ba da dadewa ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Wata matashiya mai shekaru 22 ta cika da murna yayin da ta zama mai gidan kanta a turai tun tana da kuruciyarta.
Matashiyar (@mkaythecreator) ta cika da farin ciki yayin da ta tsaya a gefen sabuwar motarta kirar Audi da ke fake a gaban gidan. Ta sanya bakar riga.
Siyan gida a Amurka
Ta fada ma mutane cewa ta karya tsiyar da ke bibiyarsu da wannan nasara. Mutane da dama a sashinta na sharhi sun cika da mamakin yadda ta yi hakan.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wasu 'yan tsirarun mutane sun bayyana cewa suna kokarin gano mai za su yi da rayuwarsu a shekaru 22. Mai gidan ta baje kolin cikin gidan a wani bidiyo.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani kan bidiyon
JBya ce:
"Ban ma san ki ba amma ina alfahari da ke kuma ina rokon Allah ya albarkace ki da karin gidaje."
Lissa Edd ta ce:
"Shekaruna 22 kuma har yanzu ina tambayar mahaifiyata me zan ci da daddaren nan."
lil.Keesha ta ce:
"Zan ci gaba da tafawa sauran mata har sau ya zo kaina."
jaylene n ta ce:
"Godiya ga Allah, na tayaki murna!"
efriyie ta ce:
"Ni a shekaru 22 ina amfani da iPhone 7."
Matashi ya fara gini bayan shekaru 5 a turai
A wani labari makamancin wannan, wani matashi 'dan Najeriya da ke zama a UK ya yi bidiyon gidan da ya yi nasarar samu daga shekaru biyar d aya yi a turai.
Mutumin (@lil.carmas.uk) ya tura kudi gida don a gina masa hadadden gida. Bidiyon nasa ya hasko yadda aikin ginin ke gudana.
Har ma ya nuna tsarin ginin da ya yi amfani da shi. Kowane kusurwa na gidan yana da ginshikan da za su iya jure nauyin ginin.
Asali: Legit.ng