Gwamnatin Kaduna Ta Dauki Hanyar Ceto Daliban da Aka Sace Zuwa Daji, Bayanai Sun Fito

Gwamnatin Kaduna Ta Dauki Hanyar Ceto Daliban da Aka Sace Zuwa Daji, Bayanai Sun Fito

  • Gwamnatin jihar Kaduna ta fara ɗaukar matakan ganin ta ceto ɗalibai aƙalla 287 da malamansu da aka sace a jihar
  • Majiyoyi sun bayyana cewa an fara tattaunawa da ƴan bindigan ta hannun wani sanannen mai shiga tsakani
  • Sace daliban dai ya girgiza ƴan Najeriya waɗanda suka yi Allah wadai kan yadda lamarin tsaro yake ƙara taɓarɓarewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - An fara tattaunawa don ganin an saƙo ɗalibai aƙalla 287 da malamansu da aka sace a ƙaramar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Jaridar The Punch ta ce wani majiya mai tushe daga gwamnatin jihar Kaduna, wanda ke da masaniya kan tattaunawar ya tabbatar da hakan.

An fara yunkurin ceto dalibai a Kaduna
Gwamna Uba Sani ya yi alkawarin ceto daliban Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Majiyar wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce gwamnatin ta fara tuntuɓar ƴan bindigan ne ta hannun wani mai shiga tsakani domin a saƙo daliban da malamansu.

Kara karanta wannan

Wasu daga cikin daliban da aka sace a Kaduna sun kubuta daga hannun 'yan bindiga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wanene mai shiga tsakanin?

Mai shiga tsakanin wanda aka sakaya sunansa dai a baya ya taka rawa wajen tattaunawa da dama da ƴan bindiga kan sace-sacen mutane.

Ƴan bindiga dai sun kai hari makarantar firamare da ke Kuriga da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar ranar Alhamis, inda suka yi awon gaba da ɗalibai da wasu malaman makarantun.

Gwamna Uba Sani, wanda ya ziyarci makarantar a ranar Alhamis, ya ba da tabbacin cewa za a kuɓutar da ɗaliban da aka sace ba tare da sun ji wani rauni ba.

Sai dai kuma, ƙasa da sa’o’i 48 da sace yaran, wanda ya jawo cece-ku-ce a ƙasar nan, wata majiya a hukumance ta ce gwamnati ta tuntuɓi ƴan bindigan domin tattaunawa a saƙo ɗaliban da malamansu.

A kalamansa:

"Gwamnati ta fara tuntuɓar ƴan bindigan don tatttaunawa ta hannun wani sanannen mai shiga tsakani. Mai shiga tsakanin shi ne ya yi ƙoƙari wajen dawo da wasu ɗalibai da aka sace shekarun baya da suka wuce.

Kara karanta wannan

Ba a gama jimamin Kaduna ba, 'yan bindiga sun sake sace dalibai a jihar Arewa

"Mai shiga tsakanin ya tattauna kan dawo da mutane da dama da aka sace a baya. Shi ne ya shiga tsakani wajen dawo da ɗaliban da aka sace a jihar Katsina shekarun baya da suka wuce.

Wasu jami’an gwamnati biyu sun tabbatar faruwar lamarin, amma sun nemi a sakaya sunansu saboda girman batun.

Sun kuma ƙi bayar da ƙarin bayani yayin da suka dage cewa yin hakan na iya kawo cikas ga ƙoƙarin da ake yi na ganin an saƙo waɗanda lamarin ya shafa tare da sanya su cikin haɗari.

Gwamnatin Kaduna ta musanta batun

A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana rahoton cewa ta ɗauki hayar wani mai shiga tsakani domin tattaunawa da ƴan bindiga domin sako ɗaliban a matsayin tsantsagwaron ƙarya.

Muhammad Lawal Shehu, Babban sakataren yaɗa labarai na Gwamna Uba Sani, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, yayin da yake mayar da martani ga rahoton jaridar.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kawo babban cikas a kokarin ceto daliban da aka sace a Kaduna

Kamar yadda jaridar The Guardian ta ruwaito, sakataren ya bayyana cewa:

"Muna so mu bayyana dalla-dalla cewa gwamnatin jihar Kaduna ba ta ɗauki wani mai shiga tsakani ba, kuma ba ma tunanin daukar irin wannan matakin.
"Ɗaukar wani mai shiga tsakani ya auku ne kawai a tunanin wakilin jaridar The Punch. Gwamnatin Jihar Kaduna tana da kyakkyawar manufa kan rashin tattaunawa da ƴan ta’adda, ƴan bindiga da sauran masu aikata laifuka."

Uba Sani ya hango kuskure wajen magance rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna, ya ce talauci da rashin tsaro sune manyan kalubalen da ke fuskantar Najeriya a halin yanzu.

Gwamnan ya bayyana cewa shugabannin siyasa a Najeriya sun biyo hanyar da ba daidai ba wajen kawo ƙarshen waɗannan manyan ƙalubalen guda biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng