‘Yan Bindiga Sun Kutsa Masallaci a Kaduna, Sun Bindige Masallata Ranar Juma'a

‘Yan Bindiga Sun Kutsa Masallaci a Kaduna, Sun Bindige Masallata Ranar Juma'a

  • 'Yan bindiga sun kai hari yayin da ake cikin sallar Juma'a a Anguwar Makera karkashin garin Kwasakwasa da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna
  • Maharan sun yi ajalin wasu masallata biyu yayin da sauran mutane suka gudu don tsira da rayuwarsu a yau Juma'a, 8 ga watan Maris
  • Hakan na zuwa ne 'yan awanni bayan harin da aka kai makarantar firamare tare da sace dalibai da malamai sama da 200 a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Kaduna - Akalla masallata biyu ne aka kashe yayin sallar Juma'a a Anguwar Makera karkashin garin Kwasakwasa da ke karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, lamarin ya afku ne da misalin karfe 2:00 na rana a ranar Juma'a, 8 ga watan Maris.

'Yan bindiga sun kai hari Kaduna
'Yan bindiga sun kashe masallata a Kaduna Hoto: @ubasanius
Asali: Twitter

Wani babba a garin, Hudu Kwasakwasa, wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce 'yan bindigar sun bude wuta akan masallata, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Yan sanda 4 sun mutu yayin da mahara suka yi ajalinsu, harin ya rusa da 'yan matansu 2

"Masallata biyu da aka kashe suna cikin sauran Musulmai da aka kai wa hari a masallacin Juma'ar a Angwar Makera lokacin da 'yan bindiga suka bude masu wuta sannan suka sace wasu a yau (Juma'a).

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"An birne mamatan a makabartar tsohuwar Kuyello."

- Hudu Kwasakwasa

'Yan bindigar sun kai farmaki ana tsaka da Juma'a

Ya ce mutane suna cikin raka'a ta biyu lokacin da aka farmake su, wanda hakan ya sa sauran mutane guduwa domin tsira da rayuwarsu.

Ya kara da cewa a 'yan kwanaki da suka gabata, 'yan bindigar sun sace kimanin mutane 9 a garin da ake kira Angwar Kanawa karkashin yankin Kwasakwasa.

Ya roki hukumomin da abin ya shafa da su kawo masu dauki, cewa 'yan bindigar na ta farmakar garuruwansu hankali kwance.

Me gwamnati da 'yan sanda suka ce kan harin?

Kara karanta wannan

Anambra: Gobara ta tashi a gidan rediyo, ta tafka barna mai yawa

Harin na baya-bayan nan na zuwa ne kasa da awanni 24 bayan 'yan bindiga sun sace dalibai sama da 287 a karamar hukumar Chikun da ke makwabtaka.

Har yanzu rundunar 'yan sanda da gwamnatin jihar basu yi martani kan lamarin ba.

Ba a samu kakakin 'yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ba a waya kuma bai amsa sakon waya da aka tura masa ba.

Remi Tinubu ta nemi a dunga kashe miyagu

A wani labarin, mun ji cewa matar Shugaban kasa Oluremi Tinubu ta bayyana masu garkuwa da mutane a matsayin matsorata. Ta jaddada cewar ya kamata duk wanda aka kama da wannan laifi ya fuskanci hukuncin kisa.

Wannan martanin na zuwa ne kan lamuran da suka faru a baya-bayan nan, da suka hada da sace mata 200 a jihar Borno da kimanin dalibai da malamai fiye da 280 a jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng