Bidiyon Wani Bahaushe Da Ya Yanka Kek Da Wayar iPhone 12 Pro Max Ya Girgiza Intanet
- Jama'a sun yi cece-kuce kan bidiyon wani matashi 'dan Arewa da ya yi amfani da wayar iPhone dinsa ta wani salo da ba a saba gani ba
- Matashin, wanda ke bikin zagayowar ranar haihuwarsa, ya yi amfani da wayarsa iPhone 12 Pro Max wajen yanka kek dinsa
- Yayin da mutane da dama suka cika da mamakin cewa ya yi amfani da tsadaddiyar waya maimakon wuka, wasu sun ga al'ajabin dalilinsa na yin haka
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Wani bidiyo da ya yadu na wani matashin Bahaushe da ya yanka kek dinsa da wayar iPhone 12 Pro Max ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.
@iphone_boy1 ne ya wallafa bidiyon a dandalin TikTok sannan ya amsa sakonni daga mutanen da suka aike masa da sakon fatan alkhairi kan zagayowar ranar haihuwarsa, wanda hakan ke nuni ga kek din shagalin ne.
A cikin bidiyon, @iphone_boy1 ya dulmiya wayar iPhone din a tsakiyan kek din don raba shi gida biyu, yayin da abokansa suka dunga kallo ba tare da sun ce uffan ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Masu amfani da soshiyal midiya sun cika da mamakin cewa kek din zagayowar ranar haihuwarsa ne ya yanka da iPhone maimakon karamin wuka.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani kan abin da matashin ya yi
aishausman969 ta ce:
"Wayar da mutane ke neman suna da shi ya kai kanka ka mayar da shi wuka sannu da kokari."
francisthomas77242455 ya ce:
"Kafin ya shirya wannan ranar kun san kwana nawa ya yi amfani da shi wajen tunanin tsawon shekarun da babu kudi kuna wajen."
Debbie ta ce:
"Suna yaudararku ne yana ta amfani da wayar wajen boye wukar da ke a daya hannun."
Khalifa ya ce:
"Ka duk masu cewa abubuwan malam bahaushe ya sha bamban, idan 'dan kudu 'dan uwanku ne ya yi za ku kira shi zolaya amma tunda 'dan Arewa ne ya yi ya zama wani abun daban, babu komai face kiyayya wawayen mutane."
Wani ya kashe abokiyar karatunsa kan iPhone
A wani labarin, mun ji cewa an kama wani matashi dan shekara 21 da ke karatu a jami’ar Adekunle Ajasin, Akungba (AAUA) Olubodun Sanni, bisa zargin kashe wata Mis Adekunle Adebisi Ifeoluwa.
An tsinci gawar Miss Adekunle a ranar 2 ga Fabrairu, 2024 a cikin wani gida mai daki daya da ta yi haya a wajen makarantar.
Asali: Legit.ng