Anambra: Gobara Ta Tashi a Gidan Rediyo, Ta Tafka Barna Mai Yawa

Anambra: Gobara Ta Tashi a Gidan Rediyo, Ta Tafka Barna Mai Yawa

  • Hukumar kashe gobara ta jihar Anambra, ta yi nasarar kashe wata gobara da ta tashi a gidan rediyon Kpakpando FM, karamar hukumar Awka
  • Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar, Engr Martin Agbili ya ce jami'ansa sun samu damar ceto wasu kayan aiki na gidan rediyon
  • Engr Agbili ya ce lamarin wanda ya faru da misalin karfe 9:30 na daren ranar Alhamis, kuma ya ya fi shafar bangaren ofisoshin ma'aikata

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Anambra - Gobara ta babbake wani gidan rediyo mai zaman kansa, Kpakpando FM, da ke garin Mbaukwu a karamar hukumar Awka ta Kudu a jihar Anambra.

Lamarin wanda ya faru da misalin karfe 9:30 na daren ranar Alhamis, an ce ya fi shafar bangaren ofisoshin ma'aikata yayin da ya kona wani bangare na dakin watsa shirye-shirye.

Kara karanta wannan

Majalisa ta fara binciken gwamnatin Buhari kan kashe N200b a shirin kidayar 2023 da aka dakatar

Hukumar kashe gobara, Anambra
Ba a samu asarar rayuka a gobarar Anambra ba Hoto: @Fedfireng
Asali: Facebook

The Nation ta ruwaito cewa ba a samu asarar rayuka a gobarar da har yanzu ba a gano musabbabin tashin ta ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda jami'an kashe gobara suka kashe wutar

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban hukumar kashe gobara ta jihar, Engr Martin Agbili ya ce jami'ansa sun ceto wasu kayan aiki na gidan rediyon.

A cewarsa:

“Da misalin karfe 9.39pm na ranar Alhamis, hukumarmu ta samu kiran gaggawa na tashin gobara a gidan rediyon Kpakpando FM, Mbaukwu.
“Nan da nan muka tura motar kashe gobara tare da jami’an mu zuwa wurin da gobarar ta tashi. Mun yi kashe kashe wutar tare da wasu kayan aiki."

Engr Martin Agbili ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Facebook na yadda jami'an hukumar suka fafata da gobarar har suka kashe ta.

Bidiyon gobarar a kasa:

Kara karanta wannan

Kaduna: 'Yan bindiga sun kai hari makaranta, sun dauke yaran firamare

Gobara ta babbaka makarantu a Anambra

A can baya, Legit ta ruwaito makamanciyar wannan gobarar da ta tashi a wasu makarantun sakandare biyu a karamar hukumar Njikoka, jihar Anambra.

Shugaban hukumar kashe gobara ta jihar, Engr Martin Agbili ya ce sun kawo kan lamarin kuma ba a samu asarar rayuka ba, sai dai lalacewar ginin makarantun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.