'Ƴan Bindiga Sun Kashe Tsohon Shugaban Hukumar Gwamnati da Wasu Mutum 2
- Wasu mahara da ake zaton ƴan fashi ne sun kashe mutum 3 ciki har da tsohon manajan darakta na hukumar gidaje ta jihar Jigawa
- Rundunar ƴan sanda ta tabbatar da faruwar lamarin a yankin ƙaramar hukumar Birnin Kudu ranar Talata da daddare
- Mai magana da yawun ƴan sandan Jigawa, DSP Lawal Shiisu, ya ce dakarun ƴan sanda sun baza komarsu domin kama maharan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Jigawa - Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta ce wasu ƴan bindiga da ake zargin ‘yan fashi ne sun kashe mutane uku a karamar hukumar Birnin Kudu.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar (PPRO), DSP Lawan Shiisu, ya fitar ranar Laraba a Dutse.
A rahoton Daily Trust, kakakin ƴan sandan ya ce:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ranar Talata mun samu labari daga kauyen Iggi cewa an ga wasu ƴan bindiga uku a kan babur ɗaya a yankin Iyayi na jihar Bauchi sun tunkaro kauyen Iggi da ke Birnin Kudu.
"Nan take aka tura ƴan sanda zuwa yankin kuma aka sanar da jami'an tsaro musamman ƴan banga. Da karfe 10:15 na dare muka sake samun rahoto daga Warwade duk a Birnin Kudu cewa waɗannan ƴan bindigar sun kwace babur."
Maharan sun kashe mutum 3
Shiisu ya ƙara da cewa maharan sun kuma buɗe wuta kan wata mota da ta tunkaro su mai ɗauke da fasinjoji huɗu.
Nan take suka kashe direban motar, Hassan Garba da fasinjoji biyu, Garba Maiwake da Shehu Saidu, rahoton Daily Post.
Mai magana da yawun ƴan sandan ya ce tuni aka ajiye gawarwakin a dakin ajiyar gawa na cibiyar kiwon lafiya ta tarayya (FMC) da ke Birnin Kudu.
A cewarsa, dakarun ƴan sanda sun bazama sintiri kurfa-kurfa da nufin cafko waɗanda suka aikata wannan ɗanyen aiki.
Hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) ta tattaro cewa direban motar, Hassan Garba, bai jima da ajiye aiki ba a Jigawa. Shi ne tsohon shugaban hukumar gidaje.
Yadda lamarin ya faru
Wani mazaunin Birnin Kudu, Malam Aminu Aminu, ya shaidawa Legit Hausa cewa abinda ya faru ya yi matuƙar tada musu hankali.
Da yake bayanin yadda lamarin ya faru yayin hira da wakilin mu, Aminu ya ce:
"Eh (Hassan Garba) baban wani abokina ne da muka yi makaranta tare, to ya je gona ya sallami waɗanda suka masa aiki, sai ya ga wasu mutane a jejin kuma dama ana masa ɓarna.
"Shi ne ya haske su da fitilar mota, to ashe ƴan iska ne, wasu na ganin Fulani ne, suka buɗe wa motar wuta, su huɗu ne a motar amma mutum ɗaya ne ya sha.
"Wanda ya tsira dabara ya yi, ya kwanta a ciki kamar ya mutu, da suka tafi shi ne ya shi ya dawo gida. Abun ba daɗi kwanta-kwata, Allah ya mana maganin su."
Yan fashi sun shiga bankuna biyu a Kogi
A wani rahoton na daban Ƴan bindiga sun farmaki ofishin ƴan sanda da bankuna biyu a jihar Kogi, sun kashe ɗan sanda ɗaya da wani bawan Allah mai talla a bakin titi
Ganau sun bayyana cewa maharan sun biyo wata motar ɗauko kudi daga wani banki, kuma sun kwashe adadi mai yawa da ba a tantance ba
Asali: Legit.ng