Ban Taba Ganin Irinsa Ba, Hadimin Tinubu Ya Fadi Lokacin da Tinubu Ke Kwanciya Duk Daren Allah

Ban Taba Ganin Irinsa Ba, Hadimin Tinubu Ya Fadi Lokacin da Tinubu Ke Kwanciya Duk Daren Allah

  • Shugaba Bola Tinubu ya samu yabo daga wurin hadiminsa kan irin yadda ya jajirce domin ganin ya inganta Najeriya
  • Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya ce bai taba ganin shugaban da ya himmatu wurin kawo sauyi irinsa ba
  • Ajuri ya bayyana haka ne a yau Alhamis 7 ga watan Maris yayin tattaunawa da matashin dan jarida, Chude Jideonwo

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – An bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin jajirtaccen shugaba wanda ya damu da matsalar Najeriya.

Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya ce Tinubu kullum baya kwanciya sai karfe biyu zuwa uku na dare.

Kara karanta wannan

Ka kula da lafiyarka madadin yawace yawace, Malamin addini ya ba Tinubu shawara

Hadimin Tinubu ya yaba masa kan fadi-tashin da yake yi domin inganta Najeriya
Ngelale ya ce ko bacci Tinubu baya iya yi domin ganin ya inganta Najeriya. Hoto: Bola Tinubu.
Asali: Twitter

Menene Ngelale ke cewa kan Tinubu?

Ajuri Ngelale ya bayyana haka ne a yau Alhamis 7 ga watan Maris yayin tattaunawa da dan jarida, Chude Jideonwo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce shi ganau ne ba jiyau ba tun da yana aiki tare da shi na tsawon lokaci kuma zai iya ba da shaidan hakan a ko wane lokaci.

“Ina aiki da mutumin da na san zan iya fadar haka a kansa saboda ya na kwanciya ne karfe biyu zuwa uku na dare har da ranakun Lahadi.
“Yana kuma tashi kullum karfe bakwai na safe zuwa takwas har da ranakun Lahadi inda zai fara bude takardun aiki har zuwa dare.
“Ma’aikaci ne na gaske kuma yana yi ne don ci gaban kasar Najeriya kamar yadda ya bunkasa jihar Legas a lokacinsa.”

- Ajuri Ngelale

Tinubu: Ajuri ya shawarci 'yan Najeriya

Kara karanta wannan

Dan Ganduje ya samu muƙami da Tinubu ya dakatar da Shugaban REA a kan N2bn

Hadimin har ila yau, ya bukaci ‘yan kasar da su marawa Shugaba Tinubu baya inda ya ce tabbas kasar ce a zuciyarsa.

Ajuri ya ce wannan halin kunci da ake ciki ya na daf da gushewa inda ya ce Tinubu ya himmatu wurin fitar da kasar a kangin da take ciki.

Tambuwal ya shawarci Tinubu

Kun ji cewa Sanata Aminu Tambuwal ya shawarci Shugaba Bola Tinubu kan halin da ‘yan kasar ke ciki.

Tambuwal ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyara gidan tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasanjo a jihar Ogun.

Ya ce tun da Tinubu ya nemi shugabancin kasar kuma ya samu, ya kamata ya yi duk mai yiwuwa domin daidaita al’amura.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.