Rai Baƙon Duniya: Daga Nada Shi Alkalin Kotu, Mai Shari'a Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Rai Baƙon Duniya: Daga Nada Shi Alkalin Kotu, Mai Shari'a Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Alkalin babbar kotun jihar Nasarawa, Mai Shari'a Tanze Benjamin Makama, ya rasu watanni biyu kaɗai bayan naɗa shi a wannan muƙami
  • Marigayi alƙalin, wanda aka naɗa ranar 29 ga watan Disamba, 2023, ya mutu ne bayan fama da rashin lafiya na ɗan ƙaramin lokaci
  • Ƙungiyar lauyoyi (NBA) reshen Ƙeffi ta yi jimamin rasuwar Makama, kuma ta aika saƙon ta'aziyya ga iyalansa da kuma babban alkalin jihar Nasarawa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Keffi, Nasarawa - Mai Shari'a Tanze Benjamin Makama, wanda aka naɗa a matsayin alƙalin babbar kotun jihar Nasarawa kwanan nan, ya riga mu gidan gaskiya.

Alkalin ya rasu ne ranar Talata, 5 ga watan Maris, 2024 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: 'Yan majalisa sun ba Tinubu shawara kan albashin da ya kamata a biya ma'aikata

Alkalin babbar kotun Nasarawa ya rasu.
Jimami Yayin da Sabon Alkalin Babban Kotu da Aka Nada Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Nasarawa Hoto: Court Of Appeal Nigeria
Asali: Twitter

Marigayi Makama ya kama aiki a matsayin alƙalin babbar kotun Nasarawa a ranar 29 ga watan Disamba, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NBA ta miƙa sakon ta'aziyya

A rahoton Sahara Reporters, rasuwar mai shari'a Makama ta jefa ɓangaren shari'a cikin alhini da jimami kuma ƙungiyar lauyoyi NBA reshen Keffi ta miƙa sakon ta'aziyya.

Nuhu J. Egya, shugaban kungiyar NBA reshen Keffi, ya bayyana mutuwar mai shari’a Makama a matsayin babban rashin ba za a iya misaltawa ba.

A wata sanarwa ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, Egya ya mika sakon ta’aziyyar ƙungiyar NBA ga iyalan marigayi alkalin, inda ya yi addu’ar Allah ya basu ikon jure wannan rashi.

Haka nan kuma ƙungiyar ta yi ta'aziyyar wannan rashi ga Mai Shari'a Aisha Bashir Aliyu, shugabar alkalan jihar Nasarawa kuma jagora a sashin shari'a.

Kara karanta wannan

Majalisa ta buƙaci Shugaba Tinubu ya gaggauta kawo ƙarshen ƴan bindiga a Jihar Arewa

Nasarawa na fama da matsaloli

Jihar Nasarawa na fama da matsloli na rashin tsaro da suka haɗa da rikicin ƙabilanci, addini da kuma rikicin siyasa mai zafi.

Ko a baya-bayan nan wasu daga cikin ƴan adawa sun yi yunƙurin tada yamutsi da sunan zanga-zanga bayan kotun ƙoli ta tabbatar da nasarar Gwamna Abdullahi Sule.

Sanusi ya yi kuka saboda mutuwar Wigwe

A wani rahoton kun ji cewa Tsohon gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi, ya fashe da kuka yayin da yake mika ta'aziyyarsa ga iyalan Herbert Wigwe.

Sanusi ya yi tsokaci a ranar Laraba, 6 ga watan Maris, yayin da yake jawabi ga taron 'yan makoki a bikin birne Wigwe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262