Saboda Mace: Malamin Addini Ya Salwantar da Ran Na Gaba da Shi a Kan Sabani
- Ana zargin Morris Fadehan, babban fasto a cocin Grace of Comfort Parish, reshen garin Ile-Ife, jihar Osun ya rasa ransa a hannun mataimakinsa
- Mai cocin, Pa Olafare, ya bayyana cewa kisan ya faru ne a sanadiyyar rikicin da ya auku a tsakanin wanda ake zargin da marigayin
- Ƴan sanda a Osun sun shiga lamarin inda suka bayyana cewa a yanzu haka lamarin na hannun sashen binciken manyan laifuka (CID)
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Ile-Ife, jihar Osun - An samu ƙarin bayani game da faston da ya kashe na gaba da shi a kwanan nan a jihar Osun.
Rahotanni da dama sun ce, Lekan Ogundipe, ya kashe Morris Fadehan, babban faston cocin Grace of Comfort Parish, a Ile-Ife.
Kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito a ranar Alhamis, 7 ga watan Maris, mai cocin, Pa Olafare, yayi ƙarin haske kan lamarin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda lamarin ya auku
Da yake jawabi a lokacin da yake tarbar wata tawaga daga cocin Celestial Church of Christ ta ƙasa, Pa Olafare ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan da mamacin ya karɓo makullan cocin daga hannun wanda ake zargin bisa cin zarafin wata fasto.
Ana zargi Ogundipe da aikata kisan a cikin cocin ba tare da an gano shi ba, rahoton Tori News ya tabbatar da batun.
Daga nan sai ya nufi gidan Pa Olafare da sauri don ya ba da labarin ya tarar da gawar Fadehan a ƙasa tana ci da wuta.
Pa Olafare ya bayyana cewa:
"Yayin da nake shirin cin abinci a yammacin ranar Litinin (26 ga watan Fabrairu) Lekan ya zo gidana ya shaida mani gawar marigayin tana ci da wuta.
"Ni da matata muka tuƙa mota zuwa cocin tare da shi inda muka tarar da wani ɓangare na gawar mamacin a ƙone.
"Sauran mambobin cocin da ke kusa su ma sun zo wurin. Lokaci da muka yi bincike a cocin, mun gano tabon jini a sassa daban-daban na jikinsa da kuma alamun an yanka shi.
"Da muka tambayi Lekan game da tabon jinin, sai ya yi yunkurin guduwa amma muka kama shi muka kulle shi a motata kafin mu kira ƴan sanda."
A halin da ake ciki, Lekan ya shaida wa ƴan sanda cewa ya aikata laifin ne saboda taƙaddamar da suka yi da marigayin.
Kisa a cocin Osun: ƴan sanda sun mayar da martani
A halin da ake ciki, Yemisi Opalola, kakakin rundunar ƴan sandan jihar Osun, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Opalola ya bayyana cewa an kama wanda ake zargin kuma an mayar da lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka na jihar (CID).
An cafke fasto a Ogun
A wani labarin kuma, kun ji cewa an cafke wani fasto a jihar Ogun ya shiga hannun ƴan sanda bisa zargin haiƙewa wata yarinya ƴar shekara tara a ɗuniya.
Fasto Timothy Adedibu ya shiga hannu ne bayan kawun yarinyar ya shigar da ƙorafi kan wannan ɗanyen aikin da ya yi mata.
Asali: Legit.ng