Tsadar Siminti: Wani Mutum Ya Kara Kudin Hayar Gidansa da Ya Gina Shekaru 30 Da Suka Wuce
- Wani 'dan Najeriya wanda ya mallaki gida ya kara kudin hayar gidansa, yana mai nuni ga kari da aka samu a farashin siminti
- Wani labari da ya yi fice wanda Fitila ya wallafa a X, ya yi nuni ga cewa gidan ba sabo bane, domin dai tun shekaru 30 da suka wuce aka gina shi
- Sai dai kuma, an ce mai gidan ya ci burin samun karin kudi daga gidan nasa yayin da farashin siminti ya yi tashin gwauron zabi
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Wani 'dan Najeriya mai gidan haya ya ce dole masu haya a gidansa su kara kudin haya saboda an samu kari a farashin siminti.
An rahoto cewa mutumin ya kara kudin hayar gidansa, yana mai nuni ga tashin farashin kayan gini kamar siminti.
Wani mai suna Fitila ne ya wallafa labarin a shafion X, inda ya ce wasu 'yan Najeriya na daga cikin masu haifar da matsalolin da ake ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kuma bayyana cewa gidan da mutumin ya kara kudin hayarsa an gina shi ne shekaru 30 da suka wuce.
Rubutun na cewa:
"Wani mai gidan haya wanda ya gina gidansa shekaru 30 da suka wuce ya kara kudin haya saboda tsadar siminti. Mu ke yiwa kanmu mugunta."
Ga wallafar a kasa:
Jama'a sun yi martani yayin da mai gida ya kara haya
@kejay_prince ya ce:
"Saboda idan yana son yin gyara, yana tafiya ne da zamani."
@IamEriOluwa ya ce:
"A'a! Mutumin da ya gina gidansa shekaru 30 da suka wuce ya zuba jari da kudinsa ne tare da fatan samun riba a jarinsa. Saboda haka, ya kara kudin haya ne domin kare kansa daga hauhawan farashin kaya da kuma samun riba mai kyau kan jarinsa."
@lecomtephyn ya ce:
"A'a yana kara kudin hayar gidan ne don shima dole ya yaki tattalin arzikin. Komai ya haura sama, kudin hayar baya biya masa bukatunsa."
Farashin siminti a kamfanin Dangote, BUA da sauransu
A wani labarin kuma, mun ji cewa Dangote, BUA, Lafarge da sauran manyan masana'antun siminti sun amince za su rage farashin siminti a Najeriya bayan wata ganawa da gwamnatin tarayya.
Taron wanda ministan ayyuka, David Umahi ya shirya, ya samu halartar ministan masana'antu, kasuwanci da zuba jari a Abuja ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu, 2024.
Asali: Legit.ng