Bidiyon ‘Dan Najeriya Da Ya Yiwa Jama'a Gwajin Jefar Da kudi Ya Ratsa Intanet
- Wani bidiyon TikTok da ya yadu ya nuno wani mutum da ke zolayar wasu mutane a titunan Najeriya ta hanyar jefar da kudinsa a kasa don ganin abin da za su yi
- Ya jefar da kudinsa da gangan a gaban wasu mabarata wadanda suka gaggauta sanar da shi cewa kudinsa ya fadi
- Sai dai kuma, lokacin da ya maimaita irin hakan a gaban wasu matasa uku da ba mabarata ba, sai daya cikinsu ya dafe kudin a sirrance
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Wani bidiyon TikTok mai ban dariya da ya hankalin masu kallo da dama ya nuno wani 'dan Najeriya da ke gudanar da bincike kan titunan kasar ta hanyar jefar da kudinsa a kasa don ganin abin da mutane za su yi.
Mutumin ya so gwadawa ya gani ko mutane za su gaggauta sanar da shi idan ya jefar da kudinsa a gabansu.
A cikin bidiyon, ya fara ajiye kudinsa a gaban wasu mabarata wadanda ke zaune a hanyar wucewa suna neman a ba su sadaka.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yaya mutane suka yi da ganin kudin?
Kamar yadda teaserprank2 ya nuna, mabaratan sun gaggauta sanar da shi cewa kudinsa ya fadi amma da bai gan su ba, sai suka kai masa kudin suka ba shi. Mutumin ya yi masu godiya sannan ya kara gaba.
Sai dai kuma, da ya maimaita irin haka a gaban wasu samari uku da ba mabarata ba, lamarin ya sauya sosai.
Daya daga cikinsu ya dafe kudin cikin dabara daga kasa sannan ya boye ba tare da ya bari mutumin ya gan shi ba.
Da mutumin ya dawo ya tambaye su ko sun ga kudin nasa, sai duk suka karyata sannan suka yi kamar ba su san abin da yake magana a kai ba. Sai mutumin ya nuna masu cewa yana daukarsu bidiyo.
Bidiyon ya haifar da martani da dama daga masu kallo wadanda suka bayyana ra'ayoyinsu game da darasin da ke tattare da zolayar.
Kalli bidiyon a kasa:
'Dan Najeriya ya yiwa mutane kyautar daloli
A wani labarin kuma, wani dan Najeriya wanda kan shirya bidiyoyin zolaya ya yi aikin alkhairi yayin da ya yi wa mutanen da bai sani ba kyautar kudi a unguwa.
Mutumin (@teaserprank_) ya shiga unguwa da daloli sannan yana ta mika su ga mutane, yana mai ce masu su karba su ji dadinsu.
Asali: Legit.ng