'Yan Ta'adda Sun Kuma Kai Kazamin Hari Kan Ƴan Gudun Hijira, Sun Dasa Bama-Bamai a Arewa
- Ƴan ta'adda da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun bankawa gidajen ƴan gudun hijira wuta a yankin Dikwa ta jihar Borno
- Mazauna yankin sun bayyana cewa ƴan ta'addan sun dasa bama-bamai a wurin aiki ginawa ƴan gudun hijira gidaje domin maida su garuruwansu
- Wani ganau ya ce da idonsa ya ga gidaje sama da 25 suna ci da wuta a kauyen Gajibo yayin da yake hanyar zuwa Maiduguri
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Borno - Wasu da ake kyautata zaton mayakan Boko Haram ne sun kona gidaje akalla 25 da aka gina wa ‘yan gudun hijira a karamar hukumar Dikwa ta jihar Borno.
Yayin da hare-haren ƴan ta'adda ke kara yawaita, mazauna Dikwa sun tsere daga gidajensu tare da fakewa a matsayin 'yan gudun hijira a cikin sabbin gidajen.
Sai dai kwanaki ƙalilan bayan sace ‘yan gudun hijirar da suka shiga daji nemo itace, ‘yan ta'addan sun kai farmaki wani kauye mai nisa a yankin Gajibo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Boko Haram ta ƙona gidajen da Zulum ke ginawa
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa daga zuwan ƴan ta'addan suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi sannan suka bankawa sabbin gidajen da aka gina wuta.
A cewar wani ganau, Modu Kundiri wanda ke kan hanyarsa ta zuwa Maiduguri daga Gomboru, sojoji sun bukaci su jira na tsawon awanni 3 a kauyen Logomani.
Mutumin ya ce:
“Sojoji sun sanar da mu cewa sai mun jira na tsawon sa’o’i 3 daga karfe 11:00 na safe zuwa 2 na rana kafin a bari mu bar Logomani.
"Na gani da idona kuma na kirga sama da sabbin gidaje 25 da aka gina a kauyen Gajibo da ke karamar hukumar Dkiwa suna ci da wuta.”
Ƴan ta'addan sun dasa bama-bamai a wurin
Wani mazaunin garin Dikwa, Sheriff Lawan, ya tabbatar da faruwar wannan labarin ta wayar tarho.
Ya kara da cewa maharan sun kuma dasa bama-bamai da dama a wurin aikin da ake yi domin dakile ayyukan sake ginawa da maida mutane gidajensu na gwamnatin Borno.
"Sojoji sun shaida mana cewa maharan sun dasa bama-bamai da dama a wurin da ake aikin, kuma tuni suka gano wasu daga ciki," In ji Sherrif.
Garin Gajibo na da tazarar kilomita 110 daga Maiduguri, babban birnin jihar Borno a Arewa maso Gabas.
Miyagun makiyaya sun kai hari a Benue
A wani rahoton kuma Wasu ƴan bindiga da ake zargin makiyaya ne sun kai mummunan hari kauyen Azandeh a karamar hukumar Ukum ta jihar Benuwai.
Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun kashe mutane da yawa cikin har ƴan uwan juna su 7, sun ƙona gidaje.
Asali: Legit.ng