Minista: Dakarun Sojoji Sun Hallaka Manyan Ƴan Bindiga 7 da Suka Addabi Mutane a Najeriya

Minista: Dakarun Sojoji Sun Hallaka Manyan Ƴan Bindiga 7 da Suka Addabi Mutane a Najeriya

  • Muhammad Badaru ya bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya na ci gaba da samun galaba kan ƴan ta'adda a faɗin Najeriya
  • Ministan tsaron ya ce a ƴan watannin da suka shuɗe, sojoji sun hallaka manyan ƴan ta'adda akalla 7 a sassa daban-daban
  • A cewarsa, sojoji na karɓan duk wanda ya tuba ya miƙa wuya yayin da masu kunnen ƙashi kuma dakaru zasu bi su har daji su kawar da su

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Ministan Tsaro, Muhammad Badaru, ya ce akalla manyan kwamandojin 'yan ta'adda bakwai ne jami'an tsaro suka kashe a cikin 'yan watannin da suka gabata.

Ministan ya bayyana haka ne ranar Talata yayin wani rangadin da ya kai hukumomin rundunar soji da kwalejin sojoji da ke Jaji a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Sojoji sun sheke shugaban ƴan bindiga da tawagarsa ta addabi jihar Katsina

Sojojin Najeriya.
Badaru: Sojoji Sun Halaka Manyan Kwamandojin Yan Ta'adda 7 a Najeriya Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Twitter

Ya ce ana samun ci gaba a yakin da ake da ‘yan tada kayar baya da kuma ‘yan bindiga da suka addabi jama'a, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Badaru ya kuma kara da cewa a yanzu ƴan bindiga sun koma kai hare-hare a shiyyar Arewa maso Yamma lokaci-lokaci ba kamar a baya ba.

Wane dabaru sojoji ke amfani su kan 'yan bindiga?

Ministan ya bayyana cewa dakarun sojoji na amfani da fasahar zamani domin gano sansanonin ‘yan ta’addan tare da kawar da su daga doron duniya.

A cewsrsa, ƴan bindiga na amfani da rashin dakarun sojoji a kowane lungu da saƙo na ƙasar nan wajen kai hare-hare kan bayin Allah.

Sai dai ya ce sojoji na ci gaba da bin ‘yan bindigar har cikin dazuka suna fatattakarsu daga wuraren da suke ɓuya, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Digiri kan Hisbah: Daurawa ya lissafa abubuwa 3 da za su yi a inganta aikinsu a Kano

Ana maraba da 'yan bindiga masu miƙa wuya

Dangane da batun tsarin bin wasu hanayoyin wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro, Badaru ya nuna cewa da yawa daga cikin ƴan ta'adda sun mika wuya.

Bisa haka, ya ce sojoji suna karban tubabbu, su sauya musu tunani kana su maida su cikin al’umma, yayin da wadanda ba sa son tuba za a ci gaba da fuskantarsu har sai an ga bayansu.

Sojoji sun daƙile yunkurin ƴan bindiga a Zamfara

A wani rahoton Dakarun sojin Operation Hadarin Daji sun halaka ɗan bindiga yayin da suka kai ɗauki kauyen Tsohuwar Tasha a ƙaramar hukumar Kaura Namoda a Zamfara

Dakarun sojojin sun samu nasarar fatattakar ƴan bindigan tare da ceto mutane 15 da maharan suka yi yunkurin yin garkuwa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262