Rayuka da Dama Sun Salwanta Yayin da Aka Samu Barkewar Mummunan Rikici, Bidiyo Ya Fito

Rayuka da Dama Sun Salwanta Yayin da Aka Samu Barkewar Mummunan Rikici, Bidiyo Ya Fito

  • An samu tashin hankali ba zato ba tsammani a yankin Ibeshe da ke jihar Legas ta yankin Kudu maso Yammacin Najeriya
  • Rikicin wanda aka yi amfani da muggan makamai, ya ɓarke ne a daren ranar Litinin, 4 ga watan Maris, kuma ya ci gaba har zuwa safiyar Talata, 5 ga watan Maris
  • Rikicin wanda ya ɓarke ya janyo asarar dukiya mai yawa tare da asarar rayukan mutane masu tarin yawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Ibeshe, jihar Legas - Rikici ya ɓarke a yankin Ibeshe da ke jihar Legas, inda wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba suka mutu, wasu da dama kuma suka jikkata.

A cewar jaridar Vanguard a wani rahoto a ranar Talata, 5 ga watan Maris, ba a san musabbabin rikicin ba wanda aka yi amfani da muggan makamai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

Kara karanta wannan

Zaman majalisa ya samu cikas yayin da aka shiga duhu, bidiyo ya bayyana

Rikici ya barke a Legas
Rayuka da dama sun salwanta a rikicin da ya barke a Legas Hoto: Benjamin Hundeyin
Asali: Facebook

Jaridar ta ruwaito wata majiya tana cewa hatsaniyar ta ɓarke ne a daren ranar Litinin 4 ga watan Maris, inda aka kwashe har zuwa safiyar Talata 5 ga watan Maris ana yinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa rikicin ya yi sanadiyyar lalata gidaje da asarar rayuka masu tarin yawa.

Majiyar ta bayyana cewa:

"Rikicin ya shafi mazauna yankin 'Ibeshe Riverside' da 'Ibeshe Seaside'.

Rikicin Ibeshe: Ƴan sanda sun maida martani

Da aka tuntubi kakakin ƴan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya bayyana cewa:

"Muna ƙoƙarin shawo kan lamarin. Mun nemi taimako daga rundunar sojojin ruwa, kuma sun haɗa kai da mu don daƙile rikicin."

Ku kalli bidiyon a nan:

Jihar Legas ba kamar sauran wasu jihohin Najeriya ba, ba a cika samun rikicin ƙabilanci ba a cikinta.

Sai dai, akwai lokutan da ake samun rikicin ƴan ƙungiyar asiri wanda yake haifar da tashin hankali sosai. Legas na ɗaya daga cikin jihohin Najeriya da ke da tsarin tsaro mai ƙarfi.

Kara karanta wannan

Ana dab da azumi, tsageru sun shiga babban Masallacin Jumu'a, sun tafka mummunar ɓarna

Rikici Ya Ɓarke a Filato

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu ɓarkewar wani sabon rikici a tsakanin mnoma da makiyaya a jihar Plateau.

Rikicin da ya ɓarke a ƙaramar Mangu ta jihar dai ya jawo ɗaruruwan mutane sun tsere daga gidajensu yayin da aka ƙona gidaje sama da 100.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng