Zaman Majalisa Ya Samu Cikas Yayin da Aka Shiga Duhu, Bidiyo Ya Bayyana
- Ƴan majalisa a majalisar dattawa sun ji takaici lokacin da suka fuskanci matsalar wutar lantarki a zamansu na ranar Talata, 4 ga watan Maris
- A cikin wani faifan bidiyo an nuna zauren majalisar cikin duhu yayin da babu kowa a kan kujeru
- Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da wata sanarwar da kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja (AEDC) ya fitar inda ta bayyana sunayen waɗanda ake bi bashi na miliyoyi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sanatoci sun jira kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja (AEDC) ya dawo da wutar lantarki kafin su fara zaman su na ranar Talata, 5 ga watan Maris 2024.
A cewar rahoton tashar Channels tv, hakan ya sa wani bangare na majalisar dattawa ya shiga cikin duhu har sai da aka dawo wutar, inda daga nan ne shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya fara zaman majalisar.
A watan Fabrairu, kamfanin AEDC ya yi gargaɗin katse wutar lantarki ga ma’aikatu da hukumomi 86 saboda wasu basussuka na N47.1bn.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma'aikatun da AEDC ya biyo bashin lantarki
Daga cikin waɗannan ma'aikatu akwai ma’aikatar kuɗi, yaɗa labarai, kasafin kuɗi, ayyuka da gidaje, barikin sojoji daban-daban, rundunar ƴan sandan Najeriya da fadar shugaban ƙasa.
Sauran sun haɗa da hukumar yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), hukumar tattara kuɗaɗen haraji ta ƙasa (FIRS) da hukumar kula da filayen jiragen sama ta Najeriya (FAAN).
Umurnin ya nuna cewa hukumomin gwamnati da ake bi basussuka dole ne su siya kuɗaɗen da ake bin su a cikin kwanaki goma, zuwa ranar 28 ga Fabrairu, 2024, ko kuma a sanya su cikin duhu.
Wani ɓangare na sanarwar cewa:
Waɗannan ma'aikatun an ba su daga nan zuwa ranar da wannan wa'adin zai ƙare nan da kwana 10 da buga wannan sanarwar, watau bayan ranar Laraba, 28 ga watan Fabrairu, 2024, za a yanke musu wuta har sai sun biya basussukan da aka biyo su."Ku kalli bidiyon a nan
Majalisa Na Shirin Cafke Shugabannin Binance
A wani labarin kuma, kun ji cewa majalisar wakilai na shirin aikewa da sammaci don cafke shugabannin kamfanin Binance.
Kwamitin majalisar kan laifukan da suka shafi kuɗaɗe ya buƙaci hakan bayan shugabannin kamfanin sun ƙi bayyana a gabansa.
Asali: Legit.ng