Ana Dab da Azumi, Tsageru Sun Shiga Babban Masallacin Jumu'a Sun Tafka Mummunar Ɓarna
- Ɓarayi sun kutsa kai cikin wani babban masallacin jumu'a a unguwar Rigasa da ke yankin ƙaramar hukumar Igabi a jihar Kaduna ranar Litinin
- Rahotanni sun nuna cewa ɓata garin sun yi amfani da mimbarin masallacin wurin sace kayayyaki da suka haɗa da fankokin da ke bada iska ga masallata
- Umar Rigasa ya shaida wa Legit Hausa cewa lamarin ya auku ne da daren Lahadi wayewar garin ranar Litinin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Rahotanni sun nuna cewa wasu ɓata gari da ake kyautata zaton ɓarayi ne sun shiga babban masallacin jumu'a da ke layin Hakimi a unguwar Rigasa.
Lamarin dai ya faru ne da daren ranar Lahadi, 3 ga watan Maris, 2024 a Unguwar Rigasa da ke yankin ƙaramar hukumar Igabi cikin jihar Kaduna.
Barayi sun shiga masallaci a Kaduna
An tattaro cewa ɓarayin sun yi amfani da munbarin liman na masallacin, suka hau suka kwance fankoki, sannan suka yi awon gaba da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani mai suna Umar Rigasa ne ya bayyana haka a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Litinin.
Ya buƙaci al'umma su taimaka su sanya ido kan hada-hadar fankokin sama ko Allah zai sa a ga waɗannan fankoki da aka sace a babban masallacin.
Wace ɓarna ɓarayin suka yi a masallacin?
Saƙon ya bayyana cewa:
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, a daren jiya Litinan wasu bata gari suka shiga cikin babban Masallacin juma'a da ke layin Hakimi Rigasa. inda sukayi anfani da munbarin Masallacin wajen hawa suka sace fankokin Masallacin.
"Don haka muna kira da jama'a su sa mana ido idan Allah yasa anga irin wadannan fankoki ga lambobin da za a kira don sanar da kwamitin wannan Masallaci. 08024770602 ko 08033500919 ko 08066000564.
"Allah Ubangiji ya tona mana Asirin wadanda sukayi wannan mummunan aikin."
Wannan na zuwa ne yayin da rage ƙasa da mako ɗaya gabanin fara azumin watan Ramadan, wata na 9 a jerin watannin kalandar Musulunci.
Legit ta tabbatar da labarin sata a masallaci
Legit.ng Hausa ta tuntuɓi Umar Rigasa kuma ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce sun wayi garin ranar Litinin da labarin sace fankokin.
Ya ce:
"Eh wannan gaskiya ne, wasu ɓata gari sun shiga babban masallacin Jumu'a na farko a Rigasa, sun ɓalle fankoki harda ta wajen liman da kuma wayoyin lasifika.
Dangane da koƙarin gano waɗanda suka aikata lamarin da kuma kwato kayan, Umar ya shaida mana cewa, "har yanzun ana dakon ko za a dace amma ba a gansu ba zuwa yanzu."
Hisbah ta kama wasu a gidan gala
A wani rahoton kuma hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kai samame wani gidan gala da aka kai masu ƙorafi a yankin ƙaramar hukar Fagge.
Yayin samamen dakarun Hisbah sun yi nasarar damƙe mutum 10 waɗanda suka kunshi mata bakwai da kuma maza guda uku.
Asali: Legit.ng