Dalla-Dalla: Ayyukan Musuluncin da Aka Kirkiri Hukumar Hisbah Domin Tayi a Jihohi

Dalla-Dalla: Ayyukan Musuluncin da Aka Kirkiri Hukumar Hisbah Domin Tayi a Jihohi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Hukumar Hisbah ta yi suna wajen tabbatar da kiyaye dokokin shari'ar musulunci, a tsakanin al'ummar musulmi, gyara tarbiyya da yaƙi da ayyukan baɗala.

Tun bayan kafa hukumar ta samar da ci gaba sosai wajen gyara tarbiyya, sulhu tsakanin al'ummar musulmai da tabbatar da bin dokokin musulunci.

Ayyukan hukumar Hisbah
Hukumar Hisbah na gudanar da ayyuka sosai Hoto: Kano Hisbah Board
Asali: Facebook

Gwamnatin jihar Kano ta kafa hukumar Hisbah a shekarar 2000, a ƙarƙashin tsohon gwamnan jihar, Rabiu Musa Kwankwaso.

Bayan jihar Kano, wasu jihohin yankin Arewacin Najeriya sun bi sahu wajen kafa hukumar Hisbah a jihohinsu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A yayin wata hira da jaridar BBC Hausa, shugaban hukumar Hisbah na Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya zayyano ayyukan da aka kafa hukumar dominsu.

Kara karanta wannan

Dan Ganduje ya samu muƙami da Tinubu ya dakatar da Shugaban REA a kan N2bn

Ga jerinsu a nan ƙasa:

1. Hisbah tana koyar da halaye masu kyau

Daga cikin ayyukan da aka ƙirƙiri hukumar Hisbah dominsu akwai koyar da al'umma halaye masu kyau.

Akwai kula da iyaye, bayar da tarbiyya ga ƴaƴa, kula da aure da dai sauransu.

2. Cika mudun awo

Hukumar tana kula da yadda ƴan kasuwa ke cika mudun awo a hatsi, mai, kayayyaki da sauran abubuwan da suka shafi aune-aune.

3. Zaburar da mutane a bada Zakkah

Hukumar ta Hisbah tana zaburar da al'umma wajen fitar da haƙƙin Allah ga waɗanda dukiyarsu ta kai su bayar da Zakkah.

4. An san Hisbah da sulhunta ma'aurata

Hukumar Hisbah tana taka muhimmiyar rawa wajen yin sulhu a tsakanin ma'auratan da suka samu saɓani a tsakaninsu.

Ta nan ɓangaren hukumar na shiga cikin rigingimun ma'aurata domin tabbatar da cewa an yi wa kowane ɓangare adalci.

5. Hisbah da masu otel

Hukumar tana kula da yadda ake bude otel da gudanar da su domin tabbatar da sun bi tsarin da bai keta dokar musulunci ba.

Kara karanta wannan

Kano: Jerin albishir 5 da Gwamna Abba ya yi wa Sheikh Daurawa da Hisbah a zaman sulhu

A wannan fannin hukumar na sanya ido wajen ganin cewa ba a sayar da giya, naman alade, hana ƙananan yara waɗanda ba su kai shekara a duniya zuwa ba tare da iyayensu ba da sauran abubuwan da ba su dace ba a irin waɗannan wuraren.

6. Taimakon jami'an tsaro

Hukumar tana taimakawa jami'an tsaro irinsu ƴan sanda da sauran hukumomin tsaro wajen gudanar da ayyukansu da suka shafi yin bincike da sauransu.

Sauran ayyukan hukumar sun haɗa da:

  • Karfafa haɗin kai a tsakanin musulmai.
  • Ƙarfafa gwiwar musulmai su haɗa kansu.
  • Bada shawara kan kiyaye cin riba.
  • Tabbatar da tsari mai kyau wajen taron addini.
  • Ƙarfafa gwiwa kan tsafta da tsaftar muhalli.
  • Sulhunta rikice-rikicen jama'a tsakanin mutane da ko ƙungiyoyi.
  • Taimakawa wajen kula da zirga-zirga.
  • Ayyukan bada agajin gaggawa

Dalilin Daurawa na komawa shugabancin Hisbah

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya yi magana kan dalilin da ya sanya ya dawo kan muƙaminsa na shugabancin hukumar Hisbah ta jihar Kano, bayan ya yi murabus.

Daurawa ya bayyana cewa ya dawo kan shugabancin hukumar ne bayan Gwamna Abba Kabir ya nemi da ya yi hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng