Gwamna Abba Ya Sasanta da Aminu Daurawa, Ya Koma Kwamandan Hisbah Gadan-gadan
- A ƙarshe, Gwamna Abba Kabir Yusuf da Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa sun sasanta kuma ya koma kujerarsa ta kwamandan Hisbah
- Wannan ya biyo bayan wata ganawa da suka yi tare da manyan malaman Kano a gidan gwamnati da daren ranar Litinin
- Sheikh Daurawa ya sanar da aje muƙaminsa ne bayan wata suka da Gwamna Abba ya yi, lamarin da ya haddasa cece-kuce a ciki da wajen Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya sasanta tsakaninsa da Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar.
Shehin malamin ya amince zai koma kujerarsa ta babban kwamandan rundunar Hisbah.
Duk da murabus din da Daurawa ya yi a wani faifan bidiyo da ya wallafa a Facebook, amma bai rubuta takardar murabus a hukumance ya mika ga hukumar da ta dace.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai a wani yunƙuri na sasanta saɓanin da ya shiga tsakani, Sheikh Aminu Daurawa tare da wasu manyan malamai sun gana da Gwamnan Kano ranar Litinin da daddare.
Shugaban na Hisbah zai koma aiki ranar Talata, kamar yadda wasu majiyoyi daga gidan gwamnati suka bayyana.
Hisbah: Daurawa ya sasanta da Abba
Kwamandan Hisbah ya tabbatar da cewa ya sasanta da Gwamna a Abba a shafinsa na dandalin Facebook, kuma ya ce zai dora daga inda ya tsaya a Hisbah.
Sheikh Daurawa ya rubuta cewa:
"Sulhu alkairi ne, Hisbah za ta ci gaba da aikinta daram, ba sani, ba sabo tare da kiyaye doka."
Yadda gwamnatin Kano ta nemi sulhu da Daurawa
An tattaro cewa tun bayan sanar da murabus, Gwamnatin Kano ta fara bin hanyoyin da suka dace domin rarrashin Sheikh Daurawa ya koma kan muƙaminsa.
Gwamnatin ta tura 'Zauren Haɗin Kan Malamai' wata tawagar manyan malaman musulunci a Kano domin su taushi zuciyar Daurawa ya koma kujerar shugaban Hisbah.
Kafin haka kuma gwamnatin Abba ta tura kakakin majalisar dokokin Kano, Jibril Falgore da babban limamin masallacin ƙasa, Abuja, Farfesa Sheikh Ibrahim Maqari, domin su shawo kan Daurawa.
Daurawa v Abba: Ko ya malamai suka ɗauki lamarin?
A wani rahoton kuma Manyan malaman musulunci sun yi maganganu kan murabus ɗin da Daurawa ya yi daga shugaban Hisbah.
Rahoton nan ya tattaro kalaman da aka ji daga bakin shugabanni da jagororin al’umma a kan sabanin da aka samu da shugaban a Hisbah.
Asali: Legit.ng