Hajj 2024: Gwamna Fintiri Ya Nada Sabon Amirul Hajj Na Jihar Adamawa, an Samu Karin Bayani
- Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya nada sabon Amirul Hajj na jihar, wanda zai jagoran alhazai zuwa sauke farali a 2024
- Fintiri a cikin wata sanarwa a ranar Litinin, ya amince da nadin Mustapha Amin, Galadiman Adamawa matsayin Amirul Hajjin bana
- Ya kuma bukaci Mustapha Amin da ya yi amfani da kwarewarsa wajen ganin al'ummar jihar sun yi aikin Hajjin ba tare da matsala ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Adamawa - Gwamna Ahmadu Fintiri na Adamawa ya amince da nadin Mustapha Amin, Galadiman Adamawa, a matsayin Amirul Hajj na aikin Hajjin 2024.
Babban sakataren yada labaran gwamnan, Humwashi Wonosikou, ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Yola, Daily Nigerian ta ruwaito.
Hajjin bana: Fintiri ya taya Mustapha Amin murna
Ya ce sauran mambobin sun hada da Farfesa Abdullahi Tukur a matsayin mataimakin shugaban tawagar, Muhammad Hammanjoda, Sheikh Musa Abdullahi da Ibrahim Abubakar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mista Wonosikou, wanda ya ambato gwamnan yana taya tawagar murna, ya bukace su da su tabbatar da sun ba maras da kunya kan wannan aiki da aka basu.
Ya kuma bukace su da su yi amfani da iliminsu da kwarewarsu wajen ganin al'ummar jihar sun gudanar da ayyukan Hajjin bana ba tare da wata matsala ba.
An samu karancin maniyyata aikin Hajjin 2024 - NAHCON
A wani labarin kuma, Legit Hausa ta ruwaito cewa hukumar alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta koka kan karancin maniyyata aikin Hajjin 2024.
Rahotanni sun bayyana cewa hukumar ta ware kujeru 70,000 ga jihohi 36 ciki har da Abuja, amma har zuwa ranar rufe biyan kudin Hajjin ba a sayar da kujerun ba.
Mafi yawan maniyyata ba su iya biyan kudin kujerun ba duk da cewa Saudiyya ta sanar da rage kudin kujerun, sai dai matsin tattalin arziki ya yi wa mutane da yawa cikas.
Kujerun Hajji 2,600 kawai aka sayar a Kano
Idan ba a manta ba, Legit ta ruwaito cewa kujerun Hajji 2,600 ne kadai aka sayar cikin 5,934 a jihar Kano, a ranar 10 ga watan Fabrairu, 2024.
Daraktan hukumar alhazai ta jihar Kano, Alhaji Laminu Rabiu ya ce har zuwa lokacin ana ci gaba da rajista da biyan kudi, wanda zuwa yanzu adadin kujerun za su iya fin 2,600.
Asali: Legit.ng