Sauƙi Ya Zo Yayin da Gwamnatin Tinubu Za Ta Fara Rabon Kayan Abinci Kyauta a Jihohin Najeriya

Sauƙi Ya Zo Yayin da Gwamnatin Tinubu Za Ta Fara Rabon Kayan Abinci Kyauta a Jihohin Najeriya

  • Ga dukkan alamu za a samu saukin wahalar da ake ciki yayin da gwamnatin tarayya ta ce za ta fara rabon kayan abinci a jihohin Najeriya
  • Ministan noma da samar da isasshen abinci, Abubakar Kyari, ya ce za a bi matakan da suka dace wajen tabbatar da tallafin ya isa ga talakawa
  • Kyari ya kuma jinjinawa ƴan Najeria bisa juriyar da suka nuna kana ya roki a ci gaba da marawa Gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Gwamnatin tarayya ƙarƙashin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, za ta fara rabon hatsi a duk fadin kasar domin rage wahalhalun da mutane ke ciki a Najeriya.

Kara karanta wannan

"Babu ruwan Tinubu" Minista ya fallasa ainihin waɗanda suka jefa ƴan Najeriya a wahala da yunwa

Ministan noma da samar da abinci, Sanata Abubakar Kyari, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na manhajar X ranar Litinin.

Gwamnatin Najeriya zata fara raba hatsi ga talakawa.
Gwamnatin Bola Tinubu Ta Shirya Fara Rabon Kayan Abinci Kyauta a Jihohi 36 Hoto: Channelstv
Asali: UGC

Kyari ya nuna tsantsar damuwarsa musamman kan mutanen da tsadar rayuwar nan ta yi tasiri a kansu, inda ya yi nuni da wawason kayan abincin da aka yi a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe za a fara rabon abinci ga talakawa?

Sai dai ya ƙara tabbatarwa ƴan Najeriya cewa gwamnatin Bola Tinubu ba ta manta da halin wahalar da mutane ke ciki ba kuma za a fara rabon kayan abinci a makon nan.

"Ina mai tabbatar muku cewa muna nan kan bakarmu ta inganta rayuwar ƴan ƙasa, za mu fara rabon tan 42,000 na hatsi a jihohi 36 cikin makon nan kamar yadda shugaban ƙasa ya bada umarni.

Kara karanta wannan

Halin Kunci: Hukumar Kwastam za ta sake rabon kayan abinci karo na 2 bisa sharuda

"Muna aiki kafada da kafada da hukumar bada agajin gaggawa NEMA da hukumar jami'an farin kaya DSS domin ganin cewa hatsin ya kai ga talakawa da aka yi dominsu kuma a kunshin da ya dace.
"Bugu da kari, za a fitar da tan 58,500 na tsabar shinkafa daga manyan injinan casar shinkafa zuwa kasuwa domin daidaita farashi."

- Abubakar Kyari.

Ministan, wanda ya yaba da juriyar ƴan Najeriya, ya bukace su da su marawa gwamnatin shugaba Tinubu baya a yunkurinta na magance kalubalen da kasar ke fuskanta.

Kyari ya ce Gwamnati karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu ta himmatu wajen magance wadannan kalubale da kuma kokarin samar da makoma mai inganci da wadata ga kowane ɗan kasa.

Me ya jawo wahala da yunwar abinci a mulkin Tinubu?

A wani rahoton kuma Ministan ayyuka ya bayyana cewa babu ruwan Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu a halin tsadar rayuwar da ƴan Najeriya suka shiga.

David Umahi ya bayyana cewa wasu abubuwa da Tinubu ya gada daga gwamnatocin baya ne suka kawo ƙarancin abinci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262