An Yiwa Jami’an ‘Yan Sanda 2 Dukan Mutuwa Saboda Dalili 1 a Jihar APC
- Wasu jami'an rundunar 'yan sanda masu kwantar da tarzoma biyu sun hadu da ajalinsu a hannun matasa a jihar Edo
- Fusatattun matasa a yankin Ikpeshi da ke karamar hukumar Akoko-Edo sun yiwa 'yan sandan dukan tsiya har sai da suka daina numfashi
- Lamarin ya faru ne bayan wata motar 'yan sanda da ke yiwa tsohon 'dan majalisa rakiya ta buge wani 'dan acaba wanda ya kai ga rasa rayuka 3
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Jihar Edo - Fustattun matasa sun yiwa wasu jami'an 'yan sanda masu kwantar da tarzoma biyu duka har lahira, sannan suka jikkata wasu biyu a Ikpeshi da ke karamar hukumar Akoko-Edo ta jihar Edo.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa matasan sun dauki matakin ne bayan wani lamari da ya faru da wata motar Toyota Hilux ta 'yan sanda da ke yiwa wani tsohon 'dan majalisar Edo, Emmanuel Agbaje rakiya.
Motar 'yan sandan ta buge wani acaba ne, wanda ya yi sanadiyar mutuwar 'dan acabar, wata mata da kuma 'danta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun bayyana cewa matasan Ikpeshi sun mamaye ofishin 'yan banga a jihar Edo, inda aka kai jami'an 'yan sandan, don haka suka sha karfinsu tare da yi masu duka har lahira.
Yadda aka ceto 'yan sanda 2 daga hannun matasa
Sai dai kuma, 'yan bangar sun ceto wasu jami'a 'yan sanda biyu, sannan suka kwato bindigoginsu.
Jami'an tsaron da aka ceto suna kwance yanzu haka a wani asibiti da ba a bayyana ba a garin Edo.
Jami'an 'yan sandan hudu sun fto ne daga sashi na 19, Port Harcourt, babban birnin jihar Ribas.
Shugaban karamar hukumar Akoko-Edo, Tajudeen Alade, wanda ya tabbatar da ayyukan matasan Ikpeshi, ya bayyana cewa za a zakulo masu aika-aikar, a kama su sannan a gurfanar da su.
Ya ce yin hakan zai zama izina ga sauran tsagerun matasa.
Rundunar 'yan sanda ta yi martani
Kakakin 'yan sandan jihar Edo, Chidi Nwabuzor, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya kuma yi bayanin cewa ana gudanar bincike kan lamarin kuma rundunar za ta saki karin bayani, rahoton Channels TV.
Matasa sun halaka hadimin Akpabio
A wani labari na daban, mun ji cewa wasu matasa sun hallaka hadimin shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio kan rabon kayan Kirsimeti.
Marigayin Ime Udoworen ya gamu da tsautsayin ne bayan an yi zargin ya handame kayayyakin da aka bayar don rabawa.
Asali: Legit.ng