An Lalata Komai a Jiha Ta Amma Ba Zan Yi Korafi Ba, Gwamna a Najeriya Ya Fadi Abin da Zai Yi a Kai
- Yayin da sauran gwamnoni ke korafi kan yadda magabatansu suke bar musu asusun gwamnati, Gwamnan Abia ya magantu
- Gwamna Alex Otti ya ce tabbas an bar masa jihar a cikin wani irin mawuyacin hali amma shi bai yi korafi ba kamar yadda saura suke yi
- Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya ke hira da gidan talabijin na Channels a makon jiya a birnin Tarayya Abuja
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Abia – Gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya bayyana yadda ya samu jihar a cikin wani irin mawuyacin hali.
Otti ya ce tsohon gwamnan jihar, Ikpeazu Okezi ya lalata komai na jihar inda ya barta a cikin wani irin mummunan yaayi.
Menene Otti ke cewa kan Abia?
Sai dai Alex ya ce ba zai yi ta magane-magane ba kan lamarin inda ya ce kawai zai yi kokarin gyara abin da ya samu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya bayyana haka ne yayin da ya ke hira da gidan talabijin na Channels a makon jiya a birnin Tarayya Abuja.
Ya ce ko kadan ba ya kushe tsarin karbar bashi babban ya abin da ya tayar masa da hankali shi ne rashin ganin abin da aka yi da kudaden, cewar Tori News.
Wane mataki Alex ya dauka kan matsalar?
A cewarsa:
“Tabbas an bar wannan jiha a cikin wani irin mummunan yanayi amma ni ba zan yi korafi ba kawai zan yi kokarin gyaran abin da na samu.
“Damuwata ba wai karbar basuka ba ne, menene aka yi da kudaden da aka karbo, idan ka samu bashin biliyan 34 a 2015 amma ka mayar da shi biliyan 192 a yanzu, banga abin da aka yi da kudaden ba.
“Baa biyan albashi ‘yan fansho na cikin mawuyacin hali makaranta da asibitoci duk sun lalace da sauran ababan more rayuwa.”
Alex ya kara da cewa idan har zaka karbi bashi amma ba ka yi amfani da shi yadda ya dace ba kawai kana cutar da jihar ce.
Harbin soji ya hallaka mutane 2
Kun ji cewa harbe-harben sojoji a jihar Delta ya hallaka mutane biyu tare da raunata wasu da dama a jihar.
Lamarin ya faru ne a jiya Asabar 2 ga watan Maris a kauyen Okere da ke karamar hukumar Warri ta Kudu.
Asali: Legit.ng