Ana Cikin Jimami Yayin da Tsohuwar Golar Tawagar Kwallon Kafar Najeriya Ta Rasu da Shekaru 30
- Ana cikin jimamin rashe-rashe a Najeriya, wata ‘yar kwallon kafar tagawar Super Falcons ta riga mu gidan gaskiya
- Marigayiyar Bidemi Aluko-Olaseni wacce tsohuwar mai tsaron gidan Najeriya ce ta rasu a yau Lahadi 3 ga watan Maris
- Aluko-Olaseni ta rasu ne bayan ta sha fama da cutar daji har na tsawon shekaru takwas kafin ta ce ga garinku
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Tsohuwar mai tsaron ragar tawagar Super Falcons ta Najeriya, Bidemi Aluko-Olaseni ta rasu ta na da shekaru 30.
Marigayiyar Aluko-Olaseni ta rasa ranta ne bayan fama da cutar daji har na tsawon shekaru takwas.
Hukumar NFF ta sanar da rasuwar Aluko-Olaseni
Hukumar Kwallon Kafar Najeriya (NFF) ita ta bayyana haka a yau Lahadi 3 ga watan Maris a shafinta na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar yayin sanar da mutuwar ‘yar wasan ta mika sakon jaje ga iyalan marigayiyar inda ta yi mata addu’ar samun rahama.
A cewar sanarwar:
“Muna alhinin sanar da mutuwar mai tsaron gidan tawagar Super Falcons, Bidemi Aluko-Olaseni bayan fama da cutar daji na tsawon shekaru takwas.
“Muna addu’ar samun rahama ga marigayiyar da kuma iyalanta domin ganin sun jure wannan rashi.”
Yadda Aluko-Olaseni ta buga wasa a Najeriya
Aluko-Olaseni ta kama kwallo a tawagar Super Falcons daga shekarar 2012 zuwa shekarar 2013 kafin kamuwa da rashin lafiya.
Har ila yau, Aluko-Olaseni ta bugawa kungiyar kwallon kafa ta Rivers Angels a gasar mata ta Firimiyar Najeriya.
Har ila yau, jarumar fina-finan Nollywood, Kate Henshaw ta rasa mahaifyarta bayan ta sha fama da jinya na tsawon lokaci.
Kenshaw ita ce mai magana da yawun kungiyar jaruman masana’antar inda ta shafe kusan shekaru 30 a matsayin jaruma.
Mista Ibu ya rasu
Kun ji cewa fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, John Okafor ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 62.
Marigayin wanda aka fi sani da Mista Ibu ya rasu ne a jiya Asabar 2 ga watan Maris a wani asibita da ake kira Evercare.
Wannan na zuwa ne bayan rasuwar wani fitaccen jarumi a jihar Osun, Quadri Sisi a ranar Juma’a 1 ga watan Maris.
Asali: Legit.ng