Najeriya ta shiga jerin kasashen da suka fi dadin zama a duniya, ita ce ta 8 a Afrika

Najeriya ta shiga jerin kasashen da suka fi dadin zama a duniya, ita ce ta 8 a Afrika

  • Wani rahoton da aka fitar ya nuna yadda ‘yan kasashen Afrika ke annashuwa da jin dadi a shekarar 2023 da ta gabata
  • An bayyana Najeriya a matsayin kasa ta takwas a wannan jeri da ke kunshe da kasashen Afrika da dama
  • Mun tattaro muku jerin kasashe 10 a Afrika da suka fi kowanne yanki dadin zama a nahiyar mai yawan al’umma

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

Najeriya ta zama kasa ta takwas a jerin kasashe ma fi dadin zama a Afirka kamar yadda rahoton dadin zaman duniya da annashuwa ya nuna a 2023.

Ya zuwa watan Maris din 2023, Finland ita ce kasa ma fi dadin zama a duniya a karo na shida a jere.

Kara karanta wannan

'Yan kabilar Igbo masu kasuwanci a jihar Arewa sun koka kan yadda ake karbar haraji a hannunsu

A Afirka, Mauritius ta zama kasa ta farko a nahiyar tare da maki 5.902. Yanayin jin dadi da annashuwa a kasar da al'adu daban-daban babu shakka sun ba da gudummawa ga wannan babban matsayi da kasar ta samu.

Najeriya ce ta 8 a kasashen da aka fi jin dadi a Afrika
Najeriya ta shiga jerin kasashen da aka fi jin dadi a Afrika | Hoto: Adekunle Ajayi/NurPhoto
Asali: Getty Images

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Algeria ita ce ta biyu a jerin, wacce ke da maki 5.392, lamarin da ke nuna kyawun kasar da ke Gabashin Afrika, rahoton The Nation.

Yadda ake samu rahoton dadin zama a duniya

Rahoton Dadin Zama na Duniya wani rahoto ne na Majalisar Dinkin Duniya da ke auna farin ciki da annashuwa a kasashen duniya.

Ana dauko bayanan ne daga Gallup World Poll, kuma sun dogara ne akan amsar da mazauna kasashen ke bayarwa game da rayuwa a cikin kasashen.

Ga dai jerin a kasa kamar yadda rahoton ya tattaro

1. Mauritius

2. Aljeriya

3. Afrika ta Kudu

Kara karanta wannan

Jerin 'yan wasan Najeriya 15 da suka fi kwasar makudan kudi a kungiyoyinsu

4. DR Congo

5. Guinea

6. Côte d’Ivoire

7. Gabon

8. Najeriya

9. Kamaru

10. Mozambique

Najeriya ce ta 17 a Afrika a 2021

Idan baku manta ba, an bayyana Najeriya a matsayin kasa ta 17 a Afrika a jerin kasashen da suka fi ko’ina dadin zama a Afrika.

Wannan na zuwa ne a cikin wani rahoton da yake bayyana Finland a matsayin kasa ta farko a jerin a matakin kasashen duniya.

Najeriya ce dai kasa mafi girma a Afrika, kuma kasar na yawan fama da ayyukan ta’addanci da cin hanci da rashawa a shekarun nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.