Sunday Igboho Ya Sharɓi Kuka Kamar Ƙaramin Yaro Da Muka Yi Magana a Waya, Lauyansa
- Yomi Aliyu, shugaban lauyoyin Sunday Igboho ya bayyana mummunan halin da wanda ya ke karewa ke ciki
- Aliyu ya ce an ɗaure Sunday Igboho cikin mari bayan an masa rauni a hannu kuma yana kuka kamar ƙaramin yaro
- Babban lauyan ya ce jakadan Nigeria a Jamhuriyar Benin, Tukur Buratai na kokarin ganin an dawo da Igboho Nigeria
Babban lauyan mai rajjin kare hakkin Yarbawa Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya bayyana irin mummunan halin da wanda ya ke karewa ke ciki a hannun yan sandan Jamhuriyar Benin, The Punch ta ruwaito.
Shugaban lauyoyin, Cif Yomi Aliyu (SAN) ya bayyana hakan ne yayin da ya yi magana da The Punch a daren ranar Talata.
DUBA WANNAN: Tsamo Ƴan Nigeria Miliyan 100 Daga Ƙangin Talauci: Har Yanzu Bamu Makara Ba – Buhari
A Jamhuriyar Benin aka tsare Igboho
Ya ce ƴan sandan na Jamhuriyar Benin sun kama Ropo, matar Sunday Igboho, sun ajiye ta a wani ɗakin ajiye wadanda ake zargi da laifi.
Ya ce:
"Sun ɗaure shi da mari a inda aka ajiye shi a Cotonou. Anyi hayaniya a filin tashin jiragen sama a lokacin da aka kama shi. Sun buge shi a hannu sannan suka saka masa ankwa a hannun, yana cikin azaba kuma yana ta sharɓar kuka tamkar yaro ƙarami a lokacin da na kira shi, na ji shi.
"Ita ma matarsa an saka ta a wani ɗaki daban amma ba a saka mata mari ba, ita ma matar tana kuka saboda yana cikin azaba. Muna addu'ar kada su biya wani ya kashe shi. Ba daidai bane ka rufe mutum sannan ka saka masa mari.
"Kun san ya ji ciwo amma ba ku kai shi asibiti ba. Mun ji cewar za a gurfanar da shi a kotu gobe ba mu san ko hakan zai yiwu ba."
KU KARANTA: Farfesa Wushishi: Abu 6 da ya kamata ku sani kan sabon shugaban NECO da Buhari ya naɗa
Idan za a iya tunawa dai an kama Igboho da matarsa ne a filin tashin jirage na Cadjehoun, Jamhuriyar Benin misalin ƙarfe 8 na daren ranar Litinin. Suna shirin shiga jirgi zuwa Jamus kafin yan sandan kasa da kasa suka kama su.
Rahotanni sun ce jakadar Nigeria a Jamhuriyar Benin, Laftanant Janar Tukur Buratai (mai murabus) yana kokarin ganin an dawo da Igboho da matarsa Nigeria.
Bai dace a mika wa gwamnatin Nigeria Igbobo ba
Amma Aliyu ya ce yarjejeniyar mayar da masu laifi kasashensu ta 1984 da Togo, Ghana, Nigeria da Jamhuriyar Benin suka rattaba hannu a kai ta bawa wadanda suka baro kasarsu saboda dalilan siyasa kariya. Ta kuma ce kada a mayar da wanda ake zargin ƙasarsa idan akwai yiwuwar ba za a yi masa adalci ba.
Azaba Na Ke Sha a Hannun DSS: Nnamdi Kanu Ya Roƙi a Tura Shi Gidan Yari
A wani labarin, shugaban na haramtaciyyar kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya roki babban kotun tarayya da ke Abuja ta tura shi gidan gyaran tarbiyya da ke Kuje a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.
Kanu, wanda aka sake kamowa sannan aka dawo da shi Nigeria a watan da ta gabata, a halin yanzu yana hannun hukumar yan sandan farin kaya, DSS.
Bayan an dawo da shi kasar Mai Shari'a Binta Nyako, wacce ta bashi beli tunda farko kan dalilin rashin lafiya kafin ya gudu a 2017, ta bada umurnin a tsare shi hannun DSS har ranar 27 ga watan Yuli.
Asali: Legit.ng