Malamin Sunday Igboho Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Bai Yi ‘Layar Zana’ Ba, Ya Bari Aka Kama Shi

Malamin Sunday Igboho Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Bai Yi ‘Layar Zana’ Ba, Ya Bari Aka Kama Shi

  • Imam Oladejo, malamin Sunday Igboho ya magantu kan dalilin da yasa Igboho bai yi layar zana ya bace daga hannun jami'an tsaro ba
  • Oladejo ya ce Sunday Igbobo ya ki bacewa ne saboda baya son jefa matarsa da al'ummar Yarbawa a cikin matsala ko rikici
  • Malamin ya kuma ce Igboho zai wuce kasar Jamus ne daga Jamhuriyar Benin sannan daga baya ya dawo Nigeria lami lafiya

Idris Oladejo, malamin Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya bayyana dalilin da yasa mai rajin kafa Kasar Yarbawan bai yi kayan zana ya bace daga hannun jami'an tsaro ba.

Da ya ke magana da The Cable a kotun daukaka kara a Jamhuriyar Benin a Kwatano, malamin da aka fi sani da Imam Oladejo, ya ce Igboho bai bace daga hannun jami'an tsaro bane saboda matarsa da Kasar Yarbawa.

Malamin Sunday Igboho Ya Bayyana Dalilin Da Yasa Bai Yi ‘Layar Zana’ Ba, Ya Bari Aka Kama Shi
Sunday Igboho da Imam Oladejo. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Ya ce:

"Sunday Igboho ya yi imani da Allah kuma ya ki jinin zalunci, musamman zaluntar yan al'ummar Yarbawa. Zai iya bacewa idan yana so, Allah ne ya bashi wannan baiwar.

Kara karanta wannan

Lauya ya bayyana laifuka 3 da gwamnatin Buhari ke tuhumar Sunday Igboho akai

"Ba zai iya bacewa ba saboda baya son jefa matarsa, da kasar yarbawa da al'ummar Yarbawa cikin matsala. Ba ya son matsala, mutum ne na gari shi yasa na ke kaunarsa."

A lokacin da jami'an tsaro suka kai samame gidan Igboho a farkon watan Yuli, an ce dan gwagwarmayar ya ce amfani da asiri ne ya bace ba su kama shi ba.

Ba za a dawo da Igboho Nigeria ba - Imam Oladejo

Oladejo, wanda ya tafi Jamhuriyar Benin tunda aka sanar cewa an kama Igbobo a ranar Litinin da ta gabata ya shaidawa The Cable cewa Igboho zai wuce Jamus daga Jamhuriyar benin kafin daga bisani ya dawo Nigeria lami lafiya.

A cewarsa:

"Na yi addu'a, na fada wa Allah na, na fada wa Ubangiji kuma Allah ba zai kunyata ni ba. Ba za a dawo da Sunday Igboho Nigeria ba.
"Daga Jamhuriyar Benin, Sunday Igboho zai tafi Jamus, sannan daga Jamus Sunday Igboho zai dawo Nigeria lami lafiya."

Kara karanta wannan

‘Muna rokon Ubangijinmu ya yi mana maganin Buhari’ - Ayo Adebanjo kan kamun Igboho

Da dama cikin magoya bayan Igboho sun tafi kotun domin ganin yadda sharia za ta kasance. Amma babu alamar cewa shi da kansa ya tafi kotun.

Lauyoyinsa sun ce za a cigaba da sauraron kararsa misalin karfe 10 ranar Litinin.

Sunday Igboho Ya Sharɓi Kuka Kamar Ƙaramin Yaro Da Muka Yi Magana a Waya, Lauyansa

A wani labarin daban, babban lauyan mai rajjin kare hakkin Yarbawa Sunday Adeyemo da aka fi sani da Sunday Igboho, ya bayyana irin mummunan halin da wanda ya ke karewa ke ciki a hannun yan sandan Jamhuriyar Benin, The Punch ta ruwaito.

Shugaban lauyoyin, Cif Yomi Aliyu (SAN) ya bayyana hakan ne yayin da ya yi magana da The Punch a daren ranar Talata.

Ya ce ƴan sandan na Jamhuriyar Benin sun kama Ropo, matar Sunday Igboho, sun ajiye ta a wani ɗakin ajiye wadanda ake zargi da laifi.

Kara karanta wannan

A kan N1000, Wani Magidanci Ya Kashe Matarsa Da Tsananin Duka a Adamawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164