‘Yar Bautar Kasa Ta Tsinci Wayar iPhone 13 Pro Max da Ta Kai Miliyan 1.3, Ta Mayarwa Mai Ita

‘Yar Bautar Kasa Ta Tsinci Wayar iPhone 13 Pro Max da Ta Kai Miliyan 1.3, Ta Mayarwa Mai Ita

  • Adedeji Taofeekat Adebimpe, wata 'yar bautar kasa a sansanin NYSC da ke Sagamu, jihar Ogun, ta tsinci wayar iPhone 13 Pro Max da ta bata
  • Wannan ya janyo mata yabo daga NYSC, ciki harda shugabar hukumar ta jihar Misis Olayinka Nasamu
  • 'Yan Najeriya a dandalin soshiyal midiya sun yaba da gaskiya da amanarta, inda wasu suka ce ta cancanci a bata aiki don ta zamo abun koyi ga saura

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Sagamu, jihar Ogun - Hukumar NYSC ta yaba ma wata 'yar bautar kasa, Adedeji Taofeekat Adebimpe, wacce ta tsinci wayar iPhone 13 Pro Max sannan ta mika shi ga mahukunta don mayar da shi ga mai ita.

Hukumar NYSC ta bayyana hakan a shafinta na X a ranar Juma'a, 1 ga watan Maris.

Kara karanta wannan

"Alkawaran iska": NLC ta mayar da martani mai zafi ga Tinubu, ta fada masa abu 1 da zai yi

'Yan Najeriya sun jinjina mata
‘Yar Bautar Kasa Ta Tsinci Wayar iPhone 13 Pro Max da Ta Kai Miliyan 1.3, Ta Mayarwa Mai Ita Hoto: @officialnyscng
Asali: Twitter

Jaridar Legit ta rahoto cewa yanzu haka Ms Adedeji na samun horo a sansanin NYSC da ke Sagamu, jihar Ogun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da take martani ga ci gaban, shugabar hukumar NYSC a jihar Ogun, Misis Olayinka Nasamu, ta yaba wa matashiyar kan zama mai gaskiya.

Ta yi kira ga sauran 'yan bautar kasa da su yi goyi da ita ta hanyar nuna dabi'un kirki a kodayaushe da kuma son juna.

Wani bincike a manhajar Jumia na siye da siyarwa a Najeriya, ya nuna cewa farashin iPhone 13 Pro Max ya fara daga miliyan 1.3 zuwa miliyan 1.7.

Jama'a sun yi martani kan gaskiyar 'yar bautar kasa

#ibn ma'aruf, @ibnmaaruf2, ya ce:

"Ya yi kyau, muna bukatar karin irin wadannan mutane a Najeriya."

Commonsense enterprise, @9nationals, ya ce:

"Abin a yaba ne sosai kyakkyawar budurwa, aiki mai kyau, kasa mai daraja. Mace don zama shugaban kasa."

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Tinubu ya tsaida ranar fara rabon abinci tan dubu 42 da jihar da za a fara

Omo Alhaji Kale , @AbdulWasihGK, ya ce:

"Wajen aiki mai kyau na jiranta, ya kamata a yaba gaskiyarta."

Saurayi ya siya wa budurwa Marsandi da iPhone 15

A wani labarin kuma, mun ji cewa wata matashiyar budurwa ta rusa ihu sannan ta kusa shidewa bayan ta ga sabuwar motar Marsandi da saurayinta ya siya mata a matsayin kyautar zagayowar ranar haihuwarta.

An saka motar kirar Marsandi a cikin wani jan kwali. Ta kusa zaucewa a lokacin da aka mika mata makullin yayin da kawayenta suka bukaci ta saita kanta wuri daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng