Labari Mai Daɗi: Gwamnan Arewa Ya Ware Naira Biliyan 4 Domin Raba Wa Ma'aikata da Ƴan Fansho
- Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe ya ware kuɗi N4.1bn domin tallafawa ma'aikata da ƴan fansho saboda tsadar rayuwa
- Wata sanarwa da ta fito daga ofishin shugaban ma'aikatan jihar Yobe, ta ce Buni ya amince da ƙarin N10,000 ga ma'aikata da N5,000 ga ƴan fansho
- Gwamnatin Yobe ta kuma ƙara yawan kudin da take warewa domin rage haƙƙin waɗanda suka yi ritaya daga N100m zuwa N200m
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Yobe - Gwamnatin jihar Yobe ƙarƙashin Gwamna Mai Mala Buni ta amince da ware zunzurutun kudi har Naira biliyan 4.1 a matsayin tallafi ga ma’aikatan jihar da ‘yan fansho.
Alhassan Sule Mamudo, mai magana da yawun ofishin muƙaddashin shugaban ma'aikatan jihar, Hamidu Alhaji ne ya bayyana haka a wata sanarwa.
Sanarwan ta bayyana cewa Gwamna Buni ya amince da ware waɗannan kuɗi ne domin tarban yanayin tsadar rayuwar da aka shiga wanda ya samo asali daga tuge tallafin mai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda Leadership ta rahoto, sanarwan ta ce:
"A kwanakin baya Mai Mala Buni ya amince da biyan N699,450,000 a matsayin tallafi ga ma’aikatan gwamnati da ‘yan fansho a tsarin biyan albashin wata-wata na ma’aikatan jiha da na kananan hukumomi.
Gwamna Buni ya ƙarawa ma'aikata albashi
Matakin ya hada da ƙarin Naira 10,000 ga ma’aikatan gwamnati da kuma N5,000 ga masu karbar fansho na tsawon watanni shida, wanda aka fara a watan da ya gabata (Fabrairu).
A cewar sanarwan, idan aka haɗa jumullar waɗannan kuɗaɗe da aka ƙara wa ma'aikata da ƴan fansho a matsayin tallafi, zai kama Naira biliyan 4.1 kenan.
Haka nan kuma gwamnatin Yobe ya waiwayi kuɗin da take warewa domin biyan gratuti ga ma'aikatan da suka yi ritaya a kowane wata, ta ƙara daga N100m zuwa N200m.
Bugu da ƙari an saki N708m domin biyan ma'aikatan kananan hukumomi da suka aje aiki, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Dattawa sun faɗi matsayarsu kan juyin mulki
A wani rahoton kuma Dattawan jihar Ekiti sun yi zaman gaggawa, sun faɗi matsayarsu kan masu kira ga sojoji su kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
A wata sanarwa da suka fitar bayan kammala taron, sun ce babu cikakken ɗan Najeriya mai kishin ƙasa da zai so sauya gwamnati ba bisa ƙa'ida ba.
Asali: Legit.ng