"Mu Ba Ƴan Siyasa Bane" Ƴan Kwadago Sun Maida Zazzafan Martani Kan Kalaman Shugaba Tinubu
- Ƙungiyar TUC ta mayar da martani ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu kan kalaman da ya yi game da zanga-zangar ƴan kwadago
- Bola Tinubu ya caccaki kungiyoyin kwadago, yana mai cewa idan mulki suke so su jira 2027, kuma ya ce ba su kaɗai ne muryar ƴan Najeriya ba
- Shugaban TUC na ƙasa, Festus Osifo, ya ce mambobinsa ba ƴan siyasa bane amma suna da ƴancin yin zanga-zanga kamar kowane ɗan kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ƙungiyar kwadago Trade Union Congress (TUC) ta mayar da martani kan kalaman da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi game da zanga-zangar da NLC ta yi.
Shugaba Tinubu ya nuna rashin jin dadinsa da zanga-zangar, inda ya ce idan mulki suke so su jira 2027 domin su shiga siyasa dumu-dumu.
A wajen kaddamar da aikin layin dogo Red Line na jihar Legas ranar Alhamis, shugaban ƙasar ya ce ƴan kwadago ba su kadai ne muryar ‘yan Najeriya ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane martani ƴan kwadago suka maida wa Tinubu?
Da yake mayar da martani ga kalaman shugaba Tinubu a cikin shirin siyasa a yau na Channels tv ranar Jumu'a, shugaban TUC, Festus Osifo, ya ce mambobin ƙungiyar ba ƴan siyasa bane.
Osifo ya bayyana cewa mambobin kungiyar TUC ba ƴan siyasa bane amma suna da damar yin zanga-zanga.
"Na saurari kalaman da ya yi a jiya inda ya ce mu jira 2027 idan muna son tsayawa takara. Zan iya yin magana da yawun ƙungiyar kwadago TUC, mu ba 'yan siyasa ba ne, mu 'yan kungiya ne.
"Muna da ƴancin yin zanga-zanga, wanda kowane dan Najeriya yana da wannan damar, Don haka ba mu da matsala da zanga-zanga. Mutane za su yi amfani da 'yancinsu a duk lokacin da suke buƙata.
"Game da batun mu jira 2027 mu shiga siyasa, bana tunanin zamu yi hakan saboda ni a matsayina babu jam'iyyar siyasar da na mallaki katin zama mamba."
"Abin da na fi maida hankali kuma nake sha'awa shi ne jin dadin membobina da ma daukacin talakawan Najeriya."
- Festus Osifo.
NLC yi raddi mai zafi ga Bola Tinubu?
A wani rahoton kuma Shugaban kasa Bola Tinubu da shugaban NLC sun yi cacar baki sakamakon halin da ake ciki na matsin rayuwa a Najeriya.
Shugaban NLC, Joe Ajaero, ya bukaci Tinubu da ya mayar da hankali wajen magance manyan kalubalen da Najeriya ke fuskanta.
Asali: Legit.ng