Fulani: Rundunar Soji Za Ta Dauki Mataki Kan Igboho Saboda Wasu Dalilai, Bayanai Sun Fito

Fulani: Rundunar Soji Za Ta Dauki Mataki Kan Igboho Saboda Wasu Dalilai, Bayanai Sun Fito

  • Rundunar sojin Najeriya ta gargadi Sunday Adeyemo kan irin kalaman da ya ke yi tun bayan dawowa Najeriya
  • Rundunar ta ce idan har abin da ya fada zai inganta tsaron kasar babu matsala amma sabanin haka kuma ya kauce layi
  • Wannan na zuwa ne bayan Igboho ya yi barazana ga Fulani wanda ya ke kiransu da makasa bayan dawowarsa Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Rundunar sojin Najeriya ta yi martani kan kalaman Sunday Adeyemo mai fafutukar kafa kasar Yarbawa.

Rundunar ta ce idan har abin da Igboho ke yi zai inganta tsaron Najeriya to ba ta da matsala da shi.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya karya gwiwar Sheikh Daurawa, ya yi murabus daga shugabancin Hisbah

Rundunar sojin Najeriya ta yi magana kan kalaman Igboho
Sojoji sun gargadi Igboho kan kalaman da ya yi game da Fulani. Hoto: Defence Headquarters, Shina Peller.
Asali: Facebook

Wane gargadi rundunar ta yi ga Igboho?

Sai dai kuma ta yi gargadi inda ta ce idan kalamansa da abin da yake yi zasu kawo cikas ga rundunar to ya kauce hanya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daraktan yada labaran rundunar, Manjo-janar Edward Buba shi ya bayyana haka yayin amsa tambayoyi ga 'yan jaridu a Abuja.

"Ban kalli bidiyon ba inda Igboho ke barazana ga Fulani da ya ke kiransu da wani makasa.
"Abin da na sani kawai shi ne mutane da al'umma duka muna maraba da su."

- Edward Buba

Ya yi alkawarin yin martani idan ya kalli bidiyon

"Idan abin da ya fada zai inganta tsaro muna maraba da hakan, amma idan ya saba tsarin rundunarmu to ya kauce hanya kuma ya saba dokar tsarin mulki.
"Duk lokacin da na kalli faifan bidiyon zan ba da martanin da ya dace."

Kara karanta wannan

Dara za ta ci gida yayin da Yarbawa suka tura gargadi ga Igboho kan wani dalili, mun samu bayanai

- Edward Buba

Idan ba a manta ba, Igboho ya yi barazana ga Fulani wanda ya ke kiransu da makasa wanda ya jawo cece-kuce a ɓangarorin kasar baki daya.

Har ila yau, Igboho ya ce zai ci gaba da gwagwarmaya don ganin yankin Yarbawa ya balle daga Najeriya yayin da ake cikin halin kunci.

Yarbawa sun gargadi Igboho

Kun ji cewa wata kungiya a yankin Yarbawa ta tura gargadi ga Sunday Igboho kan kalamansa na cin mutunci.

Kungiyar na zargin Igboho da cin mutuncin dattawan yankin wadanda suka sadaukar da rayuwarsu don ci gaban yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.